'Yan bindiga sanye da hijabi sun sace basarake a Nasarawa

'Yan bindiga sanye da hijabi sun sace basarake a Nasarawa

Wasu yan bindiga sun sace wani sarki mai daraja ta biyu a jihar Nasarawa, Abdullahi Magaji, Aron Akye na Ugah misalin karfe 7.30 na daren ranar Alhamins a garin Ugah da ke Lafiya, babban birnin jihar.

Daya daga cikin danginsa ya shaidawa Daily Nigerian a ranar Asabar cewa yan bindigan sun yi awon gaba da basaraken a kan babur kuma kawo yanzu ba a san inda suka tafi da shi ba.

Majiyar ya ce masu garkuwa da mutanen da adadin su ya tasanma 20 sun iso ne dauke da muggan makamai.

A cewar majiyar, wasu daga cikin yan bindigan sun saka hijabi, sannan suka haura katangan fadar sarkin kafin suka gano inda ya ke.

'Yan bindiga sanye da hijabi sun sace basarake a Nasarawa
'Yan bindiga sanye da hijabi sun sace basarake a Nasarawa. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Boko Haram: Shekau ya musanta rade-raden zai mika wuya, ya bada sharuddan sulhu

Masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan sarkin sun nemi a biya su kudin fansa ta Naira miliyan 50.

Majiyar ta kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun bawa sarkin dama ya yi magana da iyalansa a safiyar ranar Asabar, kwanaki biyu bayan sace shi.

"Ya kira safiyar yau ya ce suna neman a biya su Naira miliyan 50 kafin su sake shi.

"Sun tafi da wayar dansa sannan su ka kira wani lamba da suka gani a cikin wayar shi kuma ya zo ya zo gidan sarkin ya shaida musu cewa sun yi magana kuma sun ce a biya su Naira miliyan 50," a cewar majiyar.

Daily Nigerian ta yi kokarin ji ta bakin Rundunar Yan sanda game da sace basaraken amma Kakakin yan sandan, Nansel Ramhnan bai amsa wayarsa ba a lokacin da aka hada wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel