COVID-19: FDA ta amince da wani sabon maganin cutar Korona

COVID-19: FDA ta amince da wani sabon maganin cutar Korona

Cibiyar kula da abinci da magunguna ta Amurka ta bayyana magani mai suna remdesivir a matsayin maganin gaggawa a kan majinyatan Covid-19 da cutar ta tsananta a jikin su.

FDA ta ce manya da yara za su iya yin amfani da kwayar idan aka zarga ko kuma aka tabbatar da cewa suna dauke da muguwar cutar.

Shugaban FDA ya ce kwayar za ta taka rawar gani matuka ga wadanda suka fara fama da sarkewar numfashi ko kuma suke amfani da na'urar taimakon numfashi

"Ganin cewa babu wani magani tsayayye na cutar, wannan maganin zai taka rawar gani wajen rage tsananin cutar a majinyatan da ciwon ya tsananta garesu," FDA ta wallafa.

FDA ta bada wannan sanarwar ne a ranar Juma'a a yayin taron da aka yi tsakanin shugaba Donald Trump, sakataren HHS Alex Azar, kwamishinan FDA Dr. Stephen Hahn da kuma mamallakin kamfanin da ya samar da remdesivir.

COVID-19: FDA ta amince da wani sabon maganin cutar Korona
COVID-19: FDA ta amince da wani sabon maganin cutar Korona. Hoto daga Getty Images
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda wata mata ta mutu garin daukan hoto a kan dutse

Wannan hukuncin yasa likitoci za su iya fara amfani da remdesivir a kan majinyatan da cutar ta tsananta.

Da farko likitoci na amfani da maganin ne a kan gwaji amma ga majinyatan da aka rasa wanne magani zai iya taimakawa halin da suke ciki.

Amma kuma wannan ba yana nufin za a iya yi wa kowanne majinyaci amfani da maganin ba.

"Gwajin ingancin maganin da ake yi a halin yanzu ne zai sa a gane wadanne majinyata ne za su mori maganin," Schaffner ya sanar a yanar gizo.

Ana fatan nan ba dadewa kamfanin da ya samar da maganin sai samar da ruwan allurar shi. Amma akwai yuwuwar hakan ya dauka watanni ko shekaru nan gaba.

A halin yanzu, kamfanin na kokarin samar da isasshen maganin ta yadda majinyata miliyan daya za su yi amfani da shi nan da karshen shekarar 2020.

Cutar Covid-19 ta fara bulla ne a garin Wuhan da ke kasar China. Daga nan kwayar cutar ta ci gaba da yaduwa a kasashe daban-daban na duniya tare da lashe rayuka masu tarin yawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel