Annobar Corona: Babban likitan dake yaki da cutar ya kamu da ita a Legas

Annobar Corona: Babban likitan dake yaki da cutar ya kamu da ita a Legas

Bambarakwai, wai namiji da suna Hajara, a nan ma shugaban cibiyar yake da annobar Coronavirus na jahar Legas, Dakta Bowale Abimbola ne ya kamu da cutar.

Cibiyar masu kula da cutar Coronavirus dake Yaba Legas ta taka rawar gani matuka wajen yaki da annobar a jahar Legas, saboda a nan ne ake killace masu cutar.

KU KARANTA: Mutane 5 yan gida daya sun yi mutuwar ban mamaki a jahar Enugu

BBC Hausa ta ruwaito tsawon mako daya kenan da Dakta Bowale ya killace kansa, kuma rahotanni sun tabbatar da a yanzu haka yana fama da tari.

Wannan ya kara tabbatar da hatsarin da jami’an kiwon lafiya suke ciki a yayin da suke kula da masu cutar, inda zuwa yanzu jami’an kiwon lafiya 113 kenan suka kamu da ita.

Annobar Corona: Babban likitan dake yaki da cutar ya kamu da ita a Legas
Dakta Bowale Hoto: Daily Post
Asali: UGC

A jimlace, jahar Legas na da mutane 1006 da suka kamu, yayin da a Najeriya dai, cutar Coronavirus ta kama mutane 2170, 68 sun mutu yayin da mutane 351 kuma suka warke.

Jahar Kano na daga cikin jahohin da cutar ta fi kamari a yanzu biyo bayan karuwar adadin masu cutar, ko a daren alhamis an samu karin mutane 92 da suka kamu, a jimlace sun kai 311.

A wani labari kuma, Ministan kiwon lafiya a gwamnatin shugaba Buhari, Dakta Osagie Ehanire ya roki yan Najeriya su taimaka da gidajensu domin killace masu cutar Coronavirus.

Ministan ya bayyana haka ne yayin taron kwamitin shugaban kasa dake yaki da COVID-19 a Abuja, inda ya ce suna sa ran yi ma mutane miliyan 2 gwaji a cikin watanni uku masu zuwa.

Saboda haka yace akwai bukatar karin wuraren da zasu yi amfani da su domin killace mutanen da aka samu suna dauke da cutar bayan fitowar sakamakon gwaje gwajen da za’a gudanar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel