Fasto ya kamu da Coronavirus bayan ya yi ma mai cutar addu’ar samun sauki

Fasto ya kamu da Coronavirus bayan ya yi ma mai cutar addu’ar samun sauki

Gwamnan jahar Ribas Nyesom Wike ya bayyana cewa wani fasto a jahar ya kamu da cutar Coronavirus bayan ya yi ma wani mutumi dake dauke da cutar addua.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito daga cikin wadanda suka kamu da cutar har da yaran mutumin guda biyu, kamar yadda Gwamna Wike ya tabbatar.

KU KARANTA: Mutane 5 yan gida daya sun yi mutuwar ban mamaki a jahar Enugu

Sai dai gwamnan ya daura laifin yaduwar cutar a jahar ga sakacin jami’an tsaron da aka girke a iyakokin jahar don tabbatar da sun hana shiga jahar, amma su ke yi ma gwamnati zagon kasa.

“Abin da na fahimta shi ne shigo mana da cutar nan ake yi daga wajen jahar, idan aka duba karancin cutar a jahar tun daga ranar da aka fara samun bullarta, da kuma yadda take hauhawa daga baya.

Fasto ya kamu da Coronavirus bayan ya yi mai cutar addu’ar samun sauki
Nyesom Wike Hoto: Sahara Reporters
Asali: Facebook

“Muna da tabbacin idan dai ba wai an samu karin masu cutar sun shigo jahar tare da yada cutar a tsakanin al’umma bane, kamata yayi adadin masu cutar a jahar ya dinga sauka kasa, hakan ne zai bamu tabbacin kokarin da muke yi yana haifar da da mai ido.

“Misali, mutum na 7 da ya kamu da cutar ma’aikacin kamfanin hakar man fetir ne dake aiki a cikin ruwa, amma ya tafi jahar Legas ya kwana a wani Otal, daga nan ya dawo Fatakwal a ranar 9 ga watan Afrilu tare da taimakon jami’an tsaron dake gadin iyakokin jahar mu.

“Da ya fara rashin lafiya, sai aka kwantar da shi a wani asibiti mai zaman kansa, St Martin Hospital a ranar 20 ga watan Afrilu, aka kuma sallame shi a ranar 21 ga watan Afrilu.

“Kaga da’a ce jami’an tsaro sun yi aikinsu yadda ya kamata, da mutumin nan bai shigo Fatakwal dauke da cutar ba.” Inji shi.

A wani labari kuma, Ministan kiwon lafiya a gwamnatin shugaban kasa Buhari, Dakta Osagie Ehanire ya roki yan Najeriya su taimaka da gidajensu domin killace masu cutar Coronavirus.

Ministan ya bayyana haka ne yayin taron kwamitin shugaban kasa dake yaki da COVID-19 a Abuja, inda ya ce suna sa ran yi ma mutane miliyan 2 gwaji a cikin watanni uku masu zuwa.

Saboda haka yace akwai bukatar karin wuraren da zasu yi amfani da su domin killace mutanen da aka samu suna dauke da cutar bayan fitowar sakamakon gwaje gwajen da za’a gudanar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel