COVID-19: Kano ce ke jagoranci a yawan sabbin masu cutar Korona

COVID-19: Kano ce ke jagoranci a yawan sabbin masu cutar Korona

A ranar Juma'a an tabbatar da cewa an samu karin mutum 92 da suka harbu da cutar COVID-19 a jihar Kano, kamar yadda hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta bayyana.

A halin yanzu, jihar na da mutum 311 da ta tabbatar da sun kamu da cutar. Tana biye da jihar Legas mai mutum 1,006, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Amma kuma, abin na sake kamari ne a cibiyar kasuwancin arewan don ko a ranar Alhamis, mutum 80 ta tabbatar suna dauke da cutar a jihar.

A makon da ya gabata ne jihar Kano ta fuskanci koma baya wajen yakar annobar.

Dakin gwajin kwayar cutar da ke jihar ya rasa kayan aiki sannan wasu daga cikin ma'aikatan sun kamu da cutar.

Wannan lamarin yasa aka rufe dakin gwajin na wucin-gadi kafin a sake bude shi a cikin makon nan.

Hakazalika, tun bayan bullar muguwar cutar, jihar Kano ta fuskanci mace-macen manyan mutane a jihar ballantana dattijai masu shekaru daga 60 zuwa sama.

Wannan lamarin ya matukar girgiza zukatan al'umma don an fara zargin barkewar annobar a babban birnin.

A ranar Litinin din da ta gabata ne hukumar NCDC ta farfado da dakin gwajin da ya suma na kwanaki.

Yawaitar masu cutar a jihar na bayyana irin yawan samfur din da dakin gwajin ke dubawa a kowacce rana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel