Kano: Za mu wallafa hotunan masu tserewa daga cibiyar killacewa

Kano: Za mu wallafa hotunan masu tserewa daga cibiyar killacewa

Kwamitin yaki da cutar coronavirus ta jihar Kano ta ce nan ba da dadewa ba za ta wallafa hotunan mutum biyu da suka tsere daga cibiyar killacewa bayan an tabbatar da suna dauke da cutar coronavirus.

Shugaban kwamitin, Dr Tijjani Husain ya bayyana hakan a ranar Alhamis, jaridar The Punch ta wallafa.

Idan za mu tuna, mutum uku ne aka gwada kuma aka tabbatar suna dauke da cutar coronavirus a jihar Kano amma sai suka tsere.

An yi nasarar damke mutum daya amma sauran biyun har yanzu ana nemansu.

Ya ce hukuncin wallafa hotonsu ya biyo bayan kokarin da ake na ganin an kama marasa lafiyan tare da killacesu a cibiyar killacewar har sai sun warke.

Kano: Za mu wallafa hotunan masu tserewa daga cibiyar killacewa

Kano: Za mu wallafa hotunan masu tserewa daga cibiyar killacewa. Hoto daga shafin gwamnatin jihar Kano na twitter
Source: Facebook

KU KARANTA: Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza ma'adanar makaman Boko Haram a Borno (Bidiyo)

Rundunar sojin saman Najeriya ta kai wa wani yanki da mayakan Boko Haram ke amfani da shi hari.

Dakarun sun yi wa yankin Parisu da ke dajin Sambisa a jihar Borno ruwan wuta ta sama, jaridar The Nation ta gano hakan.

Wannan harin da dakarun suka kai ya tarwatsa wurin ajiyar makaman mayakan Boko Haram din.

An yi nasarar halaka wasu daga cikin 'yan ta'addan kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

Kamar yadda takardar da ta fito daga shugaban fannin yada labarai na hukumar tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya ce sun kai harin ne bayan bayanan sirrin da suka samu a kan 'yan ta'addan.

Kamar yadda takardar ta bayyana: "A cikin kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin arewa maso gabas na kasar nan, rundunar sojin saman Najeriya ta ragargaza wasu 'yan ta;adda da kuma makamansu.

"Al'amarin ya faru ne a yankin Parisu da ke dajin Sambisa na jihar Borno. 'Yan ta'adda da yawa sun rasa ransu a harin ranar 30 ga watan Afirilun 2020."

Kamar yadda yace, "An kai harin ne bayan samun bayanan sirri daga majiya mai karfi a kan harkokin 'yan ta'addan da yankin da suke."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel