Coronavirus: Gwamnatin Tarayya ta yi kira da a fara bincike domin neman maganin gida

Coronavirus: Gwamnatin Tarayya ta yi kira da a fara bincike domin neman maganin gida

Gwamnatin tarayya ta kirayi masana kimiya da masu bincike a kasar nan da su gaggauta fara bincike domin gano maganin gida da zai magance annobar cutar korona a kasar.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin yaki da da cutar korona a Najeriya, Boss Mustapha, shi ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a 24 ga watan Afrilu.

Ya ce hauhawar adadin mutanen da ke kamuwa da cutar korona a jihar Kano abin damuwa ne, amma kuma gano masu cutar wata dama ce ta rage yaduwar cutar.

Babu shakka gwamnatin tarayya ta nuna damuwa matuka dangane da likafar annobar korona ke ci gaba da yaduwar tamkar wutar daji a jihar Kano.

Baya ga annobar korona da ta yiwa jihar Kano katutu, ana kuma ci gaba da samun yawan mace-macen mutane wadda da zarce ta ko da yaushe tun daga makon da ya gabata kawo yanzu.

Sakataren Gwamnatin Tarayya; Boss Mustapha

Sakataren Gwamnatin Tarayya; Boss Mustapha
Source: Twitter

Wannan lamari ya sanya gwamnatin tarayya ta aike da tawagar kwararru domin gudanar da bincike kan musababbin da ya haifar da wannan musiba a jihar.

Haka kuma mun ji cewa Majalisar Dinkin Duniya UN da Kungiyar Lafiya ta Duniya WHO, sun tura jami'ai 3,000 jihar Kano domin bada tallafi a kan annobar korona.

KARANTA KUMA: Majalisar zartarwa ta fidda sunayen mutane 9 da suka cancanci cin gajiyar mukamin Abba Kyari

Alkaluman hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a Najeriya NCDC sun tabbatar da cewa, cikin kwanaki biyu kacal an samu sabbin mutane 118 da cutar korona ta harba a jihar Kano.

Taskar bayanai ta NCDC ta sanar da cewa an samu mutane 38 da cutar ta harba a jihar a ranar Laraba. Haka kuma cutar ta harbi wasu sabbin mutum 80 a jihar a ranar Alhamis.

Kididdigar NCDC ta tabbatar da cewa a yanzu jimillar mutanen da cutar da kama a Kano sun kai 219 yayin da tuni mutane uku suka riga mu gidan gaskiya.

Ana samun hauhawar adadin ne sanadiyar dawo da aiki a dakin gwajin gano masu cutar a jihar da aka yi kwanaki uku da suka gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel