Kare dangi: Korona ta harbi mammalakin tashar AIT, da iyalansa 7

Kare dangi: Korona ta harbi mammalakin tashar AIT, da iyalansa 7

Mammalakin kamfanin sadarwan DAAR, masu tashar talabijin AIT da Raypower, Cif Raymond Alegho Dokpesi, da iyalansa sun kamu da cutar nan ta Coronavirus.

Hakan ya faru ne kwanaki uku bayan babban dansa kuma shugaban kamfanin ya kamu da cutar.

A cewar rahoton ait.live, gwajin da hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta gudanar kan iyalin ya nuna cewa mutane takwas yan gidan sun kamu.

Tuni hukumar NCDC sun garzaya da Cif Raymond Dokpesi da iyalansa cibiyar killacewa dake asibitin koyarwan jami'ar Abuja dake Gwagwalada.

Shahrarren attajirin ya bayyanawa manema labarai cewa "Ina nan lafiya. Babu abinda nike ji."

Yanzu an kaddamar da gwajin manyan ma'aikatan tashar AIT da sukayi mu'amala da shugaban kamfanin.

Jami'an kiwon lafiya a Abuja sun garzaya hedkwatar kamfanin DAAR dake Kpaduma Hills, Asokoro domin feshe ofishoshin.

KU KARANTA: Hotunan sabon asibitin killace masu cutar Korona da jihar Legas ta bude

A bangare guda, Gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da kamuwar sabbin mutane tara da cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus a jihar ranar Alhamis, 30 ga Afrilu, 2020.

Shugaban kula da cigaban kananan asibitocin jihar, Dakta Rilwani Mohammes, ya tabbatar da hakan ga manema labarai..

Ya ce hudu daga cikinsu sun shigo jihar ne daga jihar Fatakwal da Enugu yayinda daya kuma almajiri ne da aka dawo da shi jihar.

Adadin wadanda aka tabbatar da kamuwarsu da cutar a jihar ya kai 38 kuma an sallami shida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel