An kori ma'aikata 46 a kamfanin Atiku a ranar ma'aikata ta duniya

An kori ma'aikata 46 a kamfanin Atiku a ranar ma'aikata ta duniya

Kamfanin sadarwa ta Gotel Communications mallakar tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ta sallami maaikatan ta guda 46.

Gotel Communications kamfani ne da ke watsa labarai a ta rediyo da talabijin da ke watsa labarai daga Yola, babban birnin jihar Adamawa kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito.

An mika wa maaikatan da aka kora takardar sallamarsu a ranar Jumaa wacce ta yi daidai da ranar maaikata.

Ranar Ma'aikata Ta Duniya: Atiku ya kori ma'aikata 46

Ranar Ma'aikata Ta Duniya: Atiku ya kori ma'aikata 46. Hoto daga Sahara Reporters
Source: UGC

Takardar sallamar na dauke da saka hannun babban manajan kamfanin, Mohammed El-Yakub.

Wani sashi na daya daga cikin takardar sallamar da SaharaReporters ta gani ya ce, "Kamfanin ta cimma matsayar dakatar da ayyukan da ka ke mata nan take.

"Kazalika, za a lissafa dukkan hakokin ka da albashi a tura maka zuwa asusun ajiyar bankin ka nan take."

Ranar Ma'aikata Ta Duniya: Atiku ya kori ma'aikata 46

Ranar Ma'aikata Ta Duniya: Atiku ya kori ma'aikata 46. Hoto daga Saharareporters
Source: UGC

Idan ba a manta ba a baya wasu maaikata yan kasar waje sun zargi kamfanin Gotel da saba dokokin kwangilar su da kuma rashin biyansu albashi na watanni da wasu allawus.

Yan kasashen wajen sun yi barazanar za suyi karar kamfanin a kotu saboda saba yarjejeniyar kwangilarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel