Sabbin Mutane 9 sun kamu da Coronavirus a Bauchin Yakubu

Sabbin Mutane 9 sun kamu da Coronavirus a Bauchin Yakubu

- Jihar Bauchi ta samu karin masu cutar Korona

- Da cikinsu akwai ma'aikatan kiwon lafia biyar

- Yanzu adadin wadanda suka kamu da cutar a Bauchi ya kai 38

Gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da kamuwar sabbin mutane tara da cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus a jihar ranar Alhamis, 30 ga Afrilu, 2020.

Shugaban kula da cigaban kananan asibitocin jihar, Dakta Rilwani Mohammes, ya tabbatar da hakan ga manema labarai..

Ya ce hudu daga cikinsu sun shigo jihar ne daga jihar Fatakwal da Enugu yayinda daya kuma almajiri ne da aka dawo da shi jihar.

Adadin wadanda aka tabbatar da kamuwarsu da cutar a jihar ya kai 38 kuma an sallami shida.

Dakta Mohammed yace: "Muna da ma'aikata kiwon lafiya biyar da suka kamu da cutar. Sannan akwai almajiri daya da wasu mutane uku da suka dawo daga Fatakwal da Enugu."

Kwamishanan lafiyan jihar, Dakta Aliyu Maigoro, ya ce tuni an killace wasu mutanen da suka dawo da jihohon RIvers da Enugu.

KU KARANTA: Yabon gwani ya zama dole: Jahohi guda 3 da suka ciri tuta wajen yaki da COVID19 a Najeriya

A bangare guda, Majalisar dinkin duniya da kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta tura jami'ai 3,000 jihar Kano don bada tallafi a kan annobar korona.

Shugaban kwamitin fadar shugaban kasa a kan yaki da cutar, Boss Mustapha, ya sanar da hakan yayin jawabi a garin Abuja a yammacin Juma'a.

Mustapha, wanda shine sakataren gwamnatin tarayya ya ce martanin gwamnatin tarayya ya fara kawo nasara a jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel