Mutane 5 yan gida daya sun yi mutuwar ban mamaki a jahar Enugu
Jama’an unguwar Amaokpo na kamar hukumar Enugu ta gabas sun tashi cikin tashin hankali a ranar Alhamis bayan sun tarar da gawarwakin wasu mutane biyar yan gida daya.
Punch ta ruwaito an wayi gari an tarar da gawar maigidan mai suna Onyekwere Chukwumalu tare da iyalinsa su biyar ne a cikin dakinsu, kwance gefe da gefe.
KU KARANTA: Coronavirus: Ganduje ya yi fatali da asibitin da Kwankwaso ya bai wa gwamnatin Kano
Tun ranar Litinin aka musu ganin karshe, babu wanda ya san halin da suke ciki a cikin gidan har sai da wani abokin Onyekwere ya je nemansa a gidan, daga nan ne ya sanar da makwabta.
Abokin ya tafi gidan ne don haduwa Onyekwere, amma sai ya ga gidan a kulle, ga kuma motarsa a waje, don haka ya matsa gaba dakin, daga nan ya hangi gawarwakinsu.
Daga nan ya sanar da makwabta wanda suka fasa kofar, sa’annan suka kira jami’an United Nation Rescue Mission da suka kwashe gawarwakin zuwa dakin ajiyan gawa na asibitin garin.
Shaidan gani da ido ya bayyana cewa akwai yaron Onyekwere guda daya dan shekara 10 da ya tsallake rijiya da baya, kuma a yanzu yana samun kulawa a babban asibitin Ituku-Ozala.
jama'a da dama sun bayyana alhinin mutuwar Onyekwere, mutumin da suka bayyana shi a matsayin mutumin kirki dake zaman alfiya da kowa.
Kwamandan rundunar United Nation Rescue Mission Emmanuel Okoye ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai ya koka kan yadda Yansanda suka ki amsa kiran da aka musu.
Sai dai wasu makwabtan mamatan na ganin kamar guba suka ci a cikin abinci duba da yadda fatar jikinsu ta fara zagwanyewa, kuma ga shi basu da janareta balle a ce hayakin janareta ne.
Ko da aka tuntubi kakaakin Yansandan Enugu, Daniel Ndukwe-Ekea game da lamarin, sai yace ba shi da masaniya, amma zai bincika ya ji gaskiyar lamarin.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng