Ku taimaka da gidajenku don killace masu cutar Coronavirus – Ministan Buhari ga yan Najeriya

Ku taimaka da gidajenku don killace masu cutar Coronavirus – Ministan Buhari ga yan Najeriya

Ministan kiwon lafiya a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dakta Osagie Ehanire ya roki yan Najeriya su taimaka da gidajensu domin killace masu cutar Coronavirus.

Punch ta ruwaito ministan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a taron kwamitin shugaban kasa dake yaki da COVID-19 a ranar Alhamis a Abuja.

KU KARANTA: Coronavirus: Ganduje ya yi fatali da asibitin da Kwankwaso ya bai wa gwamnatin Kano

A yayin taron daya gudana a ofishin hukumar kiyaye yaduwar cututtuka, NCDC, Ministan ya ce suna sa ran yi ma mutane miliyan 2 gwaji a cikin watanni uku masu zuwa.

Ku taimaka da gidajenku don killace masu cutar Coronavirus – Ministan Buhari ga yan Najeriya

Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Saboda haka yace akwai bukatar karin wuraren da zasu yi amfani da su domin killace mutanen da aka samu suna dauke da cutar bayan fitowar sakamakon gwaje gwajen da za’a gudanar.

“Ina rokon yan Najeriya su bayar da gidajensu na dan wani lokaci saboda wannan aiki, ina fatan mutane da dama zasu bayar da gidajensu ga gwamnatocin jahohi saboda aikin.

“Ba wai mun rasa wuri bane a yanzu, amma muna wannan kiran ne saboda gaba, don ya kasance mun kammala shiri.” Inji shi.

Ministan ya kara da cewa a yanzu haka ana tattaunawa game da alawus din ma’aikatan kiwon lafiya dake yaki da COVID-19, saboda hadarin da suke ciki, amma banda jami’an tsaftar muhalli.

Daga karshe ya bayyana cewa akwai cibiyoyin gwajin cutar Corona a Najeriya guda 25, kuma a kowacce rana suna yi ma mutane 2500 gwaji, don haka ya nemi yan Najeriya su je a musu gwaji.

A wani labarin kuma, Gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana dalilin sa narokon shugaba Buhari ta sassauta ma jama’an Kano dokar hana fita da ta kakaba musu.

Aranar Alhamis ne Ganduje ya yi wannan kira yayin da yake rantsar da wani kwamitin kwararru da za su taimaka ma kwamitin yaki da COVID19 na jahar Kano.

A jawabinsa, Ganduje ya roki Buhari ya rage kwanaki 14 da ya sanya ma jahar Kano na ba shiga ba fita, saboda a cewarsa hakan zai rage wahalhalu a jahar, musamman a watan Ramadan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel