Labari mai dadi: Kano za ta fara sallamar wadanda suka warke daga cutar Korona

Labari mai dadi: Kano za ta fara sallamar wadanda suka warke daga cutar Korona

Wasu daga cikin majinyatan cutar korona a jihar Kano sun warke kuma za a fara sallamarsu, in ji mataimakin Gwamna, Dr Nasiru Yusuf Gawuna.

Dr Gawuna ne shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 ta jihar Kano kuma shi ya sanar da wannan labarin mai dadi.

Ya sanar da hakan ne da yammacin ranar Alhamis a yayin da yake bayanin a kan inda aka kwana game da cutar a jihar.

Ya ce wasu daga cikin majinyata sun samu sakamakon gwajinsu na farko kuma yana nuna basu dauke da cutar.

Amma kuma ya ce dole ne a bi duk wasu matakai na sallamar majinyatan don tabbatar da sun rabu da muguwar cutar kafin su hadu da 'yan uwansu.

Shugaban kungiyar martanin gaggawa, Dr Tijjani Husseni ya tabbatar da cewa mutum biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar a jihar Kano.

Kamar yadda jaridar Daily Trust tace, ya bayyana cewa akwai shirye-shiryen samar da karin dakunan gwajin kwayar cutar a jihar.

Labari mai dadi: Kano za ta fara sallamar wadanda suka warke daga cutar Korona

Labari mai dadi: Kano za ta fara sallamar wadanda suka warke daga cutar Korona. Hoto daga shafin twitter na gwamnatin jjihar Kano
Source: Twitter

KU KARANTA: Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza ma'adanar makaman Boko Haram a Borno (Bidiyo)

Husseni wanda ya ce gudun masu cutar da ake yi ya zama babban kalubale, ya yi kira ga gwamnati da ta kara wayar wa da jama'a kai a kan cutar don kowa zai iya samunta.

A halin yanzu, Gwamna Ganduje ya rantsar da kwamitin mutum 7 wanda ya kunshi kwararru don taimakawa kwamitin yakar cutar na jihar.

A wani labari na daban, hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta ce dakin gwajin coronavirus na biyu a jihar Kano ya kammala.

Hukumar ta sanar da hakan ne ta shafinta na twitter a ranar Alhamis. Hukumar ta ce dakin gwajin na nan a jami'ar Bayero da ke Kano.

"Dakin gwaji na 18 a kasar nan ya kammala a jami'ar Bayero da ke Kano. Shine na biyu a jihar.

"Mun mayar da hankali wajen samar da dakunan gwajin cutar kamar yadda dabarun gwaji suka bayyana," wallafar tace.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa an shirya dakin gwajin ne inda zai iya gwada samfur 180 a kowacce rana don taimakawa dakin gwajin da ke asibitin koyarwa na Aminu Kano.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, hukumar jami'ar ta sanar da shirin ta na fara gwajin cutar coronavirus a ranar 1 ga watan Mayu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel