Yadda wata mata ta mutu garin daukan hoto a kan dutse

Yadda wata mata ta mutu garin daukan hoto a kan dutse

Wata mata mai shekaru 31 da zame da fado kasa daga dutse mai nisar kafa 115 ta mutu yayin da ta ke tsayuwar daukan hoto a kasar Turkey.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi bayan gwamnatin kasar ta dage dokar kulle da ta saka a kasar saboda bullar coronavirus kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kazakh yar asalin Olesya Suspitsyna ta mutu a gaban kawarta da ke daukan ta hoto a birnin Antalya da ke Kudu maso yammacin kasar kamar yadda Daily Mail ta ruwaito.

Matan biyu sun tafi sanannen wurin shakatawa na Duden Park makonni kadan bayan dage dokar hana fitar kuma a nan ne Olesya ta ce za ta dauki hoto a kusa da wani dutse inda korammar ruwa ke gudana a bayan ta.

Yadda wata mata da mutu garin daukan hoto
Yadda wata mata da mutu garin daukan hoto. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: FG ta umarci ma'aikata da su koma bakin aiki, ta saka rana

Ta hau kan dutsen ta fara tsaya kawar ta na daukan ta hoto amma daga bisani ta taka ciyawa ta zame ta fado daga dutsen bai nisar mita 35 da mutu.

Cikin dimuwa, kawarta ta kira masu taimakon gaggawa. Daga bisani an ciro gawar Olesya daga cikin ruwa. Yan sanda sun yi bincike sun gano cewa tsautsayi ne ya yi sanadin mutuwar ta.

Kawayan Olesya sun bayyana bakin cikinsu tare da yi wa iyalan ta taaziya a dandalin sada zumunta.

A cewar wata aminiyar Olesya, Olga Kravchuk:

"Olesya tana kaunar teku kuma tana sha'awar rayuwa a Turkey. Kafin rasuwarta ta cimma wannan burin. Fiye da komai, tana son yanci. Wannan babban rashi ne. Zuciya ta ta karaya."

Olesya ta ta yi aiki a matsayin mai yi wa masu yawon bude ido jagora na tsawon shekaru biyar. Za a tafi da gawarta zuwa Kazakhstan a ranar Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel