Kwankwaso ya bukaci SSS da gwamnatin Kaduna su ceto Dadiyata

Kwankwaso ya bukaci SSS da gwamnatin Kaduna su ceto Dadiyata

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta hannun hukumar yan sandan farar hula, SSS, da gwamnatin jihar Kaduna su kara kaimi domin ceto magoyin bayansa, Abubakar Idris da aka fi sani da Dadiyata.

Daily Trust ta ruwaito cewa an sace Dadiyata ne a gidansa da ke Kaduna misalin karfe 1 na daren ranar 2 ga watan Agusta a wani yanayin mai ban tsaro kuma har yanzu ba a gano inda ya ke ba.

Dadiyata, mai shekaru 34 da haihuwa malami ne da ke koyarwa a Jamiar Tarayya da ke Dutsin Ma a jihar Katsina kuma ya dade yana sukar tsare tsaren gwamnati a kafafen sada zumunta.

Iyalan sa sun yi karar SSS da akafi sani da DSS, Kwamishinan Yan sandan jihar Kaduna da Gwamnatin jihar game da bacewarsa.

Kwankwaso ya bukaci SSS da gwamnatin Kaduna sun ceto Dadiyata

Kwankwaso ya bukaci SSS da gwamnatin Kaduna sun ceto Dadiyata. Mallakin Hoto: Daily Trust
Source: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: FG ta umarci ma'aikata da su koma bakin aiki, ta saka rana

Amma hukumar ta DSS a cikin wata wasika da ta aike wa Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta ce ba ta san inda ya ke ba kuma ba ita ta sace shi ba.

A bangarensa, Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, DSP Sabo ya bayar da tabbacin cewa yan sanda na iya kokarin su domin gano inda Dadiyata ya ke.

A hirar da Kwankwaso ya yi da Dele Momodu a Instagram ya ce gazawar hukumomin tsaro na ceto Dadiyata ya nuna akwai gyara da ya dace a yi a bangaren, inda ya kara da cewa Dadiyata dan Najeriya ne na gari mai son gaskiya.

Tsohon gwamnan kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya yace, "An sace daya daga cikin magoya bayan mu, dan Najeriya na gari kuma malami a Jamiar Tarayya ta Dutsinma a jihar Katsina a gidansa a gaban iyalansa tun shekarar da ta gabata amma har yanzu babu wanda ya ganshi.

"Mun yi iyaka kokarin mu musamman ta hannun hukumar SSS amma har yanzu ba mu gano inda ya ke ba.

"Yanzu ina amfani da wannan damar wurin kira ga gwamnatin tarayya, gwamatin jihar Kaduna da dukkan masu ruwa da tsaki suyi duk mai yiwuwa don ganin an dawo da shi wurin iyalansa"

A hirar bidiyon da aka gudanar kai tsaye, an tattauna abubuwa da dama da suka shafii jihar Kano da kasa har da batun annobar coronavirus da dokar kulle a Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel