Yadda Madagascar ke yaki da Coronvirus: 128 sun kamu, 92 sun warke babu wanda ya mutu

Yadda Madagascar ke yaki da Coronvirus: 128 sun kamu, 92 sun warke babu wanda ya mutu

Yayin da kasashen duniya ke jiran manyan kasashen duniya su binciko maganin Coronavirus da fatan maganin ya yi aiki, wata karamar kasa a nahiyar Afirka ta yi gaban kan ta.

Wannan kasa ita ce Madagascar, tsibiri ce a cikin tafkin Indian Ocean dake da nisan kilomita 400 daga yankin gabashin Afirka, al’ummar kasar sun kai miliyan 26 a kidayan shekarar 2018.

KU KARANTA: Coronavirus: Ganduje ya yi fatali da asibitin da Kwankwaso ya bai wa gwamnatin Kano

Madagascar ta binciko wani magani na gargajiya daga wani ganye wanda ta sarrafa shi kamar ganyen shayi, kuma ta sanya masa suna COVID-Organics.

A ranar Litinin, 20 ga watan Afrilu shugaban kasar Madagascar, Andry Rajoelina ya kaddamar da maganin, wanda da shi suke amfani wajen magance cutar Coronavirus.

Maganin COVID-Organics ya warkar da mutane 92 daga cikin mutane 128 da suka kamu da cutar a kasar, 36 suka rage, kuma ba’a samu mutum daya da ya mutu sakamakon cutar ba.

A cewar shugaba Rajoelina: “Duk wasu gwaje gwajen magungunan sun kammalu, kuma an tabbatar da karfinsa wajen kashe duk wasu almomin cutar Coronavirus a jikin dan Adam, don haka mun amince da shi a matsayin maganin COVID19 a Madagascar.”

Cibiyar bincike ta Malagasy ce ta binciko maganin COVID-Organics, kuma yana kunshe da sinadarin Artemisia, wani ganye a kasar da suke amfani da shi wajen yaki da cutar Malaria.

Hakan ta sa karamin ministan lafiya na kasar Equatorial Guinea, Mitoho Ondo’o ya kai ziyara kasar Madagascar, inda ya kwashi maganin da yawa da nufin warkar da jama’an kasar su.

Amma har yanzu majalisar kiwon lafiya ta duniya, WHO, na cigaba da gargadin cewa har yanzu ba’a samu maganin COVID-19 ba, don haka jama’a su daina amfani da maganin da baba tabbas.

Ita ma kwalejin likitanci ta kasar Madagascar, Anamem ta bayyan shakku game da ingancin maganin, inda ta gargadi jama’a daga amfani da shi saboda babu tabbacin maganin na aiki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng