Coronavirus: Gwamna Lalong ya daga ma jama’an Filato kafa na kwanaki 3
Gwamnatin jahar Filato a karkashin jagorancin Gwamna Simon Lalong ta sanar da sassauta dokar hana shige da fice da ta sanya a jahar don gudun yaduwar annobar Coronavirus.
Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana Lalong ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, inda yace ya bai wa jama’a hutun kwanaki 3 daga ranar Alhamis zuwa ranar Lahadi.
KU KARANTA: Coronavirus: Ganduje ya yi fatali da asibitin da Kwankwaso ya bai wa gwamnatin Kano
Gwamnan yace ya yi hakan ne domin jama’a su samu daman sayen kayan abinci kafin dokar ta cigaba da aikinta, kamar yadda ta faro daga ranar 23 ga watan Afrilu da 26.
“Dokar ta baci da muka sanya a daren Lahadi, 26 ga watan Afrilu zuwa 30 ga watan Afrilu za mu sassauta shi daga ranar 30 ga watan Afrilu zuwa 3 ga watan Mayu domin jama’a su sayi abinci. Don haka dokar za ta cigaba da aiki daga ranar Litinin, 4 ga wata.
“Haka zamu cigaba da gudanar da tsarin dokar, ta yadda a duk sati za’a iya fita daga ranar Alhamis har zuwa ranar Lahadi domin sayen kayan abinci.” Inji shi.
Gwamnan ya nanata matsayar gwamnatin na hana tafiye tafiye tsakanin jaha da jaha, ko kuma daga wata karamar hukuma zuwa wata karamar hukuma, sai dai ga wadanda aka kebance.
“Muna kira ga manoma su tabbata sun yi noman su a cikin yankunansu, hakan ya zama wajibi don dakile yaduwar cutar Coronavirus, tare da saukaka tsarin binciko wadanda aka yi mu’amala dasu.” Inji shi.
A wani labarin kuma, Gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana dalilin sa narokon shugaba Buhari ta sassauta ma jama’an Kano dokar hana fita da ta kakaba musu.
A ranar Alhamis ne Ganduje ya yi wannan kira yayin da yake rantsar da wani kwamitin kwararru da za su taimaka ma kwamitin yaki da COVID19 na jahar Kano.
A jawabinsa, Ganduje ya roki Buhari ya rage kwanaki 14 da ya sanya ma jahar Kano na ba shiga ba fita, saboda a cewarsa hakan zai rage wahalhalu a jahar, musamman a watan Ramadan.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng