COVID-19: Jihar Kano ta samu dakin gwaji na biyu

COVID-19: Jihar Kano ta samu dakin gwaji na biyu

Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa ta ce dakin gwajin coronavirus na biyu a jihar Kano ya kammala.

Hukumar ta sanar da hakan ne ta shafinta na twitter a ranar Alhamis. Hukumar ta ce dakin gwajin na nan a jami'ar Bayero da ke Kano.

"Dakin gwaji na 18 a kasar nan ya kammala a jami'ar Bayero da ke Kano. Shine na biyu a jihar.

"Mun mayar da hankali wajen samar da dakunan gwajin cutar kamar yadda dabarun gwaji suka bayyana," wallafar tace.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa an shirya dakin gwajin ne inda zai iya gwada samfur 180 a kowacce rana don taimakawa dakin gwajin da ke asibitin koyarwa na Aminu Kano.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, hukumar jami'ar ta sanar da shirin ta na fara gwajin cutar coronavirus a ranar 1 ga watan Mayu.

Farfesa Isa Abubakar, daraktan hukumar kula da cutuka masu yaduwa da bincike na jami'ar, ya ce suna shirin samar da dakin gwajin tun kafin bullar cutar.

COVID-19: Jihar Kano ta samu dakin gwaji na biyu

COVID-19: Jihar Kano ta samu dakin gwaji na biyu. Hoto daga jaridar guardian
Source: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Kasashe 5 da cutar Korona ta fi tsananta, yawan mace-mace da waraka

Abubakar yace rashin sukuni ne yasa basu kammala samar da dakin gwajin ba.

"Karfin iya gwaji da yawan da za ta iya gwadawa ya zarce na dakin gwajin jihar. An samar da dabarun shawo kai tare da mu'amala da samfur masu yawa," yace.

Ya tabbatar da cewa cibiyar za ta fada neman riga-kafi bayan ta samu kayan aiki cikakku.

Kamar yadda yace, jami'ar na da hali da kuma kayan aikin da za ta yi amfani dasu wurin samo riga-kafin Covid-19.

Cutar Korona ta fara bulla ne a garin Wuhan da ke kasar China, amma ta ci gaba da yaduwa zuwa wasu kasashen duniya.

A halin yanzu cutar ta taba kasashe da yankuna 212 na duniya. Mutum 3,308,678 ne cutar ta damka a fadin duniya.

Ta kashe mutum 234,123 inda mutum 1,042,991 ne suka tashi daga jinyar muguwar annobar, kamar yadda worldometer.info ya bayyana.

A kowacce rana, ana ci gaba da samun bazuwar cutar a kasashen duniya. Amma kuma ana samun sauki a wasu kasashen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel