Sojoji sun kama Kanal da Manjo na bogi a Legas

Sojoji sun kama Kanal da Manjo na bogi a Legas

Hukumar sojin kasan Najeriya, ta samu nasarar cafke wasu sojojin bogi guda 13 da suka shafe tsawon shekaru goma sha biyu suna tsula tsiyarsu a birnin Iko na jihar Legas.

Daga cikin sojojin bogin wadanda dubunsu ta cika har da Laftanar Kanal Afolabi Hassan da kuma Manjo Afolabi Allen Adegboyega da suka shafe shekaru su na sheke aya a matsayin manyan hafsoshin soji.

Dakarun leken asiri na rukunin bataliyar sojin kasan ta 81, su suka yi ruwa da tsaki wajen cafke sojojin na bogi kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

Babban hafsin sojan da ke jagorantar rukunin batalaiyar sojin kasan ta 81, Manjo Janar Olu Irefin, ya ce an samu nasarar cafke miyagun ne biyo wani bincike da tattaro bayanan sirri.

Manjo Olu ya ce tun binciken farko aka gano cewa daya daga cikin sojojiin na bogi mai shiga a matsayin babban hafsi wato Kanal Hassan, ya na tsula tsiya tun a shekarar 2008 kuma a baya an taba kama shi da laifin.

Shugaban hafsin sojin kasan Najeriya; Tukur Buratai

Shugaban hafsin sojin kasan Najeriya; Tukur Buratai
Source: Twitter

Kwamandan ya ci gaba da cewa, babu shakka dokar kulle da ka shimfida a jihar Legas sanadiyar annobar korona ta taimaka a yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin bankado miyagun sojoji masu saba doka.

KARANTA KUMA: Kusan duk wadanda cutar korona ta kama za su warke - NCDC

Ya ce "a yanzu mun samu nasarar cafke sojojin bogi guda 13 tun da dokar hana fita ta fara aiki."

"Za mu ci gaba da tatsar bayanai a wurinsu musamman domin sanin wajen wanda suke samun kayan kaki na sojoji gabanin mu mika su ga hukumar 'yan sanda."

Haka kuma daya sojan bogin mai shekaru 52 da ya ke shige da fice da mukamin Manjo, wato Afolabi Allen, ya na amfani da wannan dama ta tsoratar da masu barazanar kwace masa filaye da gonaki a jihar Ogun.

Sauran sojojin bogin 'yan ku ci ku bamu da suka shiga hannu sun hadar da; Joseph Okere, Emmanuel Akpaka, Frank Eze, Ahmed Ameh, Sunday Olawale, Siasia Sunday, Festus Nwanozie, Ebenezer Adeleke, Joseph Gabriel, Ibe Eze da kuma Joel Akpan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel