COVID-19: Kasashe 5 da cutar Korona ta fi tsananta, yawan mace-mace da waraka

COVID-19: Kasashe 5 da cutar Korona ta fi tsananta, yawan mace-mace da waraka

Cutar Korona ta fara bulla ne a garin Wuhan da ke kasar China, amma ta ci gaba da yaduwa zuwa wasu kasashen duniya.

A halin yanzu cutar ta taba kasashe da yankuna 212 na duniya.

Mutum 3,308,678 ne cutar ta damka a fadin duniya. Ta kashe mutum 234,123 inda mutum 1,042,991 ne suka tashi daga jinyar muguwar annobar, kamar yadda worldometer.info ya bayyana.

A kowacce rana, ana ci gaba da samun bazuwar cutar a kasashen duniya. Amma kuma ana samun sauki a wasu kasashen.

Akwai kasashen da cutar ta fi kamari kuma ta fi halaka jama'a. Wadannan kasashen su ne:

1. Amurka

Kasar Amurka ce take da kusan kashi daya bisa uku na mutanen da suka kamu da muguwar annobar. Mutum 1,095,210 ne suka kamu da cutar Korona a kasar Amurka.

Majinyata 155,737 ne suka warke daga cutar yayin da mutum 63,861 suka ce ga garinku sakamakon cutar.

2. Spain

A fadin duniya, kasar Spain ce ke biye da Amurka a yawan mutanen da suka kamu da cutar. Mutum 239,639 ne jimillar wadanda cutar ta kama.

Mutum 137,984 suka warke daga jinya yayin da mutum 24,543 suka riga mu gidan gaskiya.

COVID-19: Kasashe 5 da cutar Korona ta fi tsananta, yawan mace-mace da waraka
COVID-19: Kasashe 5 da cutar Korona ta fi tsananta, yawan mace-mace da waraka. Hoto daga Aljazeera
Asali: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram: Bana bukatar dakarun Najeriya su sassautawa 'yan ta'adda - Buhari

3. Italy

Kasar Italy ta matukar girgiza da wannan annobar, amma kasashen Amurka da Spain sun sha gabanta a halin yanzu.

Mutum 205,463 ne suka harbu da cutar a kasar. An samu warakar mutum 75,945 yayin da mutum 27,967 suka rasa rayukansu.

4. Ingila

Ingila ce kasa ta hudu da cutar ta fi kamari a duniya. Ta kama mutum 171,258 amma mutum 26,771 sun ce ga garinku sakamakon annobar.

5. Faransa

Kasar Faransa ce ta kasance kasa ta biyar a duniya da muguwar cutar ta fi yi wa illa. Cutar ta damki mutum 167,178 sannan a hankali mutum 49,476 suka warke.

An samu rashin rayuka har 24,276 sakamakon annobar a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel