Likitoci sun firgita da al'amarin jihar Kano

Likitoci sun firgita da al'amarin jihar Kano

Akwai yuwuwar samun koma baya a yakar annobar korona a jihar Kano sakamakon ja da baya da likitoci suke yi a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano.

Likitocin sun koka da rashin kayan kariya, lamarin da suka tabbatar da cewa yana jefe su a hadarin harbuwa da cutar.

Likitocin da ke rukunin masu neman kwarewa a asibitin, sun samu kan su a cikin mawuyacin hali, musamman ta yadda marasa lafiya suke karuwa a asibitin.

Sakamakon samun karuwar mace-mace a jihar, al'amarin na matukar ta'azzara.

Shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa na reshen asibitin Mallam Aminu Kano, Dokta Abubakar Nagoma ya ce aikin da suke yi ya karu, amma kuma suna fama da karancin kayan kariya.

"Muna cikin hadari don marasa lafiya na karuwa kullum. Aiki ya tsaya cak saboda bamu san me zamu taba ko gani ba," cewar Dokta Abubakar.

Kamar yadda yace, hukumomi a asibitin sun yi matukar kokari wurin samar da takunkumin fuska, safar hannu da sinadarin tsaftace hannu amma kuma babu kayan kariya.

Don haka, ya zama dole likitocin su ja da baya don karin kare lafiyarsu da ta iyalansu da abokan aikinsu.

Hakazalika, hukumomi a asibitin Mallam Aminu Kano sun tabbatar da cewa suna matukar fuskantar kalubale.

Likitoci sun firgita da al'amarin jihar Kano
Asibitin Mallam Aminu Kano. Hoto daga hotel.ng
Asali: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Yadda cutar Korona ta kashe basarake mai daraja ta farko a Borno

Shugaban sashen ba da magani na asibitin, Farfesa Musa Babashani, ya shaidawa BBC irin matsanancin halin da suke ciki.

"Kasar nan da duniya baki daya na fama da rashin kayan aiki, amma hukumar asibiti da na Annabi na kawo agaji," yace.

Ya ce tallafin da ake samu ba isa suke yi ba amma sun tattauna da kwamitin gwamnatin tarayya domin nemo mafita.

Asibitin Mallam Aminu Kano dai ya zama da'ira ta yadda jama'a ke tururuwar zuwa neman magani. Ba daga sassan kasar nan kadai ba, har da kasashe masu makwabtaka.

Durkushewar asibitin kuwa zai zama babban kalubale musamman a yanzu da ake rufe asibitocin kudi da ke fadin kasar nan sakamakon annobar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel