Ganduje ya nemi a sassauta dokar kulle jihar Kano

Ganduje ya nemi a sassauta dokar kulle jihar Kano

A daren ranar Alhamis ne gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta sassauta dokar kulle Kano na tsawon sati biyu da ta saka.

Ganduje ya ce ya yi kira a kan a sassauta dokar ne saboda halin matsin tattalin arziki da jama'a ke ciki, musamman a cikin wannan wata na Azumi.

"Za mu shigo da kwamitin shugaban kasa na kar ta kwana a kan annobar covid-19 (PTF) domin neman izininsu a kan sassauta dokar kulle Kano.

"Mu na yin wannan kira ne da yawun jama'ar Kano, wanda yanzu haka su ka fara fuskantar matsalar karancin kayan abinci a gidajensu.

"Mu na son gwamnatin tarayya ta sassauta dokar domin jama'a su samu damar sake sayen kayan abincin da za su ajiye a gidajensu, musamman a wannan lokaci da mafi yawan mutane su ke azumi.

"Yin hakan zai kawo saukin matsin tattalin arziki da ake fuskanta yanzu haka a jihar Kano," a cewar Ganduje.

Ganduje ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a gidan gwamnatin Kano yayin rantsar da mambobin wani kwamiti da zai taimakawa kwamitin kar ta kwana a kan annobar covid-19 a jihar Kano.

Ganduje ya nemi a sassauta dokar kulle jihar Kano
Gwamna Ganduje
Asali: Twitter

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta na kara fadada aiyukan kiwon lafiya domin samun damar duba adadin ma su dauke da kwayar cutar covid-19, wanda ke cigaba da hauhawa a jihar.

Farfesa Musa Borodo ne shugaban kwamitin da gwamna Ganduje ya rantsar a gidan gwamnatin Kano.

DUBA WANNAN: An sake kama 'yan gudun hijira a cakude da dabbobi suna kokarin shiga Kaduna daga Kano (Hotuna)

Kwamitin, mai mambobi 7, zai taimakawa kwamitin kar ta kwana na Kano wajen samar da hanyoyin da za a kawo karshen kwayar cutar covid-19 a jihar.

Kazalika, shugaban kwamitin kar ta kwana a kan covid-19 na jihar Kano, Dakta Tijjani Hussain, ya ce, ya zuwa yanzu, annobar ta kashe jimillar mutane 5 ne kadai a jihar.

Dakta Tijjani ya kara da cewa babu wani mai dauke da kwayar cutar covid-19 da ya mutu a cibiyar killacewa ta jihar Kano.

A cewar Dakta Tijjani, kwanan nan za a sallami wasu da ke zaman jinyar cutar covid-19 bayan an tabbatar da samun saukinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel