Ramadan: Amfanin Azumi ga lafiyar dan Adam

Ramadan: Amfanin Azumi ga lafiyar dan Adam

Baya ga falala mai tarin yawa da dumbin lada ribi-ribi kamar yadda Allah Madaukakin Sarki ya fada, azumi yana kuma da wasu sirrika na bunkasa lafiyar bil Adama.

Wasu daga cikin hikimomin shar’anta Azumi sun hadar da:

1 – Tabbatar da tsoron Allah, wajen amsa wa umarninsa, da biyayya ga shari’arsa. Allah Madaukakin Sarki ya ce, “(An wajabta muku azumi ne) ko kwa samu tsoron Allah” (Suratul Baqara : 183).

2 – Saba wa kai hakuri, da karfafa wa zuciya wajen danne sha’awa.

3 – Saba wa mutum da kyautatawa, da jin tausayin mabukata da talakawa, saboda idan mutum ya dandani yunwa zuciyarsa za ta yi laushi ta karkata zuwa ga mabukata.

4 – Samun hutu a jiki da samun lafiya a cikin azumi.

A binciken da aka wallafa cikin wata mujallar kiwon lafiya ta jami'ar Swami Vivekanand Subharti da ke kasar India, an wassafa jerin alfanun azumi ga lafiyar dan Adam.

Musulmi a duniya su na gudanar da azumin farilla na tsawon wata guda a kowace shekara ta kalandar musulunci cikin watan Ramadan.

Ma’anar Azumi a Shari’a shi ne bautawa Allah ta hanyar kamewa daga cin abinci da abin sha da jima’i, tun daga hudowar Al fijir har zuwa faduwar rana.

Buda bakin azumi

Buda bakin azumi
Source: UGC

Duk da wasu na ganin cewa akwai wahala mutum ya hana kansa ci da sha na tsawon sa'o'i yayin azumi, sai dai binciken masana ilimin kimiyya ya tabbatar da akwai wasu tarin sirrika na bunkasa lafiya da azumi ya kunsa.

1. Rage yawan sikari daga jikin dan adam: Azumi yana hana mutum kamuwa da ciwon suga mafi muni wanda a turance ake kira Diabetes Melitus. Azumi yana kone sunadarin Calorie wanda ke janyo hadarin kamuwa da ciwon suga.

KARANTA KUMA: Jihohi 35 da aka samu bullar cutar Covid-19 a Najeriya - NCDC

2. Kona kitse da rage teba: Babu shakka azumi kan taimaka wajen rage teba da kone kitse. Hakan ya sanya masu tumbi da nauyin jiki ke jin dadin jikinsu a lokacin azumi. Yana karawa na'urorin dake narkar da abinci karko.

3. Tsaftace jiki da hutar da sassan jiki: A sanadiyar hutar da sassan jiki da tsaftace su, azumi kan hana tsufa da wuri kuma mutum ya dade cikin koshin lafiya.

4. Inganta lafiyar kwakwalwa: Azumi na kara karsashi da lafiyar jiki, hakan na sanya nagartar sinadarin jiki wanda ke taimako wajen kara kaifin kwakwalwa.

5. Inganta garkuwar jiki da hana kasala: Azumi kan kara lafiyar na’urar jiki mai isar da duk wani sako wadda turance ake kira Hormone.

6. Inganta lafiyar zuciya: Sanadiyar kone kitse da azumi ya ke yi, al'amarin da ke daidaita hawa da saukar jini, hakan yana inganta lafiyar zuciya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel