Tamola a zamanin Coronavirus: An nada kungiyar PSG zakarun gasar Ligue 1 na kasar Faransa

Tamola a zamanin Coronavirus: An nada kungiyar PSG zakarun gasar Ligue 1 na kasar Faransa

Hukumar shirya gasar kwararrun yan kwallon kafa ta kasar Faransa ta sanar da kungiyar Paris Saint-Germain, PSG, a matsayin wadanda suka lashe gasar kakar kwallon bana.

Kamfanin dillancin labaru na AFP ta ruwaito a lokacin da aka dakatar da gasar a watan Maris, PSG ne ke kan gaba a jadawalin gasar da maki 12, fiye da kungiyar Marseille.

KU KARANTA: Mace mace a jahar Kano: Mutane 2 sun mutu dalilin cutar Coronavirus

An dakatar da gasar ne biyo bayan barkewar annobar Coronavirus a kasar, wanda ta kashe kimanin mutane 24,000 a fadin kasar Faransa.

Wannan tasa aka kawo karshen gasar da duk wasu gasar wasannin motsa jiki sakamakon hadarin da hakan ka iya jefa jama’a da masu gudanar da gasar da kuma kasar gaba daya.

An kawo karshen gasar kakar kwallon kafa na bana ne bayan Firai ministan kasar Faransa, Edouard Phillipe ya bayyana cewa:

Tamola a zamanin Coronavirus: An nada kungiyar PSG zakarun gasar Ligue 1 na kasar Faransa
PSG Hoto: Goal
Asali: Getty Images

“Ba zai yiwu a cigaba gudanar da duk wasu gasar kwararru na motsa jiki, musamman kwallon kafa ba, saboda hadarin hakan.”

Biyo wannan cigaba da aka samu, an sanar da PSG a matsayin wanda ta lashe gasar na shekarar 2019-2020, kuma za’a bata kofin ta.

Shugaban gasar kwallon kafa ta Faransa, Didier Quillot ya bayyana cewa zuwa 25 ga watan Mayu zasu sana da hukumar UEFA kungiyoyin da zasu wakilceta a gasar zakarun nahiyar turai.

A wani labarin kuma, hukumar majalisar UN dake kula da yawan al’ummar duniya, UNFPA, ta bayyana cewa za’a samu juna biyu da ba’a shirya daukan su ba guda miliyan 7 a fadin duniya.

UNFPA ta ce idan aka kara wata 6 a cikin dokar hana fita, za’a samu kimanin mata miliyan 47 a kasashe masu tasowa da ba zasu iya samun hanyoyin da suke bi wajen hana daukan ciki ba.

Saboda haka UNFPA ta tabbatar da cewa sakamakon binciken da ta yi ya nuna mata fiye da miliyan 7 za su iya samun juna biyu sakamakon halin kulle da rashin fita da ake ciki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel