Da duminsa: Mun fara fuskantar karancin gadajen ajiye masu cutar Korona a Legas

Da duminsa: Mun fara fuskantar karancin gadajen ajiye masu cutar Korona a Legas

Cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta ce ta fara fuskantar barazanar karancin gadajen kwantar da wadanda suka kamu da cutar Korona a jihar Legas.

Shugaban cibiyar na NCDC, Dakta Chikwe Iheakwaezu, ya bayyana hakan ne a hira da manema labarai da kwamitin kar ta kwanan fadar shugaban kasa na yakar cutar Coronavirus.

Jihar Legas ce jiha mafi yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya.

Kawo yanzu, mutane 947 ne suka harbu da cutar a jihar, duk da cewa 187 sun samu waraka kuma an sallamesu.

Chikwe Iheakweazu ya bayyanawa manema labarai ranar Alhamis cewa suna iyakan kokarinsu wajen ganin cewa an samar da isassun gadajen kwantar da sabbin masu cutar.

A cewarsa: "Legas kadai ce jihar da muke fama da karancin gadajen asibiti yanzu. Ba zamu gushe muna fadawa yan Najeriya gaskiya ba. Muna fuskantar barazanar karancin gadaje a Legas yanzu."

Asibitoci ukun da ake kwantar da masu cutar Coronavirus a jihar Legas sune IDH Yaba, asibitin koyarwan jami'ar Legas LUTH, Idi Araba; sannan cibiyar killacewar filin kwallon Onikan.

Ihekwaezu ya ce hukumarsa ta dau sabon salon gwajin mutane ta hanyar bi gida-gida, saboda haka yana kira ga yan Najeriya su baiwa jami'an gwamnatin hadin kai.

KU KARANTA: An sake kama 'yan gudun hijira a cakude da dabbobi suna kokarin shiga Kaduna daga Kano

A wani labarin daba, A yau Alhamis, gwamnatin jihar Legas ta sanar da sallamar majinyata 12 dake fama da cutar Coronavirus a cibiyoyin killacewarta bayan sun samu waraka.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Legas, Gboyega Akosile, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.

Ya ce mutane 12 da aka sallama sun hada da maza tara da mata uku. Daya daga cikinsu bature ne dan kasar Ukraniya.

Ya kara da cewa an sallami shida daga asibitin jinyar cututtuka dake Yaba, biyar daga asibitin jami'ar Legas LUTH, sannan daya daga Ibeju-Lekki.

Yanzu adadin wadanda jihar Legas ta sallama bayan fama da cutar Korona ya kai 199.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel