Jihohi 35 da aka samu bullar cutar Covid-19 a Najeriya - NCDC

Jihohi 35 da aka samu bullar cutar Covid-19 a Najeriya - NCDC

A karo na farko kenan Najeriya ta samu sabbin mutane 196 da suka kamu da cutar toshewar kafofin shakar iska wato coronavirus a ranar Laraba, 29 ga Afrilun 2020.

Wannan adadi na sabbin mutanen da annobar ta harba shi ne mafi rinjaye ta fuskar yawa da aka samu a rana daya a Najeriya, tun bayan da cutar ta fara bulla a kasar.

A halin yanzu an samu bullar cutar covid-19 a jihohi 35 na Najeriya ciki har da babban birnin tarayya kamar yadda kididdigar alkaluman hukumar dakile cututtuka masu yaduwa NCDC ta tabbatar.

Taskar bayanai ta NCDC a ranar Laraba 29 ga watan Afrilun 2020, ta ce cutar corona ta harbi mutane 1728 yayin da tuni mutum 307 suka warke tun bayan bullarta a kasar.

Jadawalin NCDC ya tabbatar da cewa cutar corona ta hallaka mutum 51 a fadin kasar.

Alkaluman da NCDC ta wallafa sun nuna a jihar Legas kadai sabbin mutane 87 sun kamu, yayin da aka samu mutu 24 a Kano. Sai kuma jihar Gombe inda aka samu mutum 18 da kuma Kaduna mai mutum 17.

Sabbin mutanen da cutar ta harba a birnin tarayya Abuja sun kai 16, inda Katsina ta samu mutum 10, yayin da birnin Shehu wato Sokoto aka samu mutum 8.

A jihar Edo an samu mutum 7, sai kuma jihar Borno da ta biyo baya da mutum 6 yayin da jihohin Adamawa da Ebonyi inda aka samu mutum daya a kowanensu.

Jihar Yobe wadda aka samu bullar cutar karon farko ita ma tana da mutum daya da ya kamu.

Likafar annobar cutar korona na ci gaba a Najeriya duk da irin kai komo da mahukuntan lafiya ke yi babu dare babu rana domin dakile yaduwarta a kasar.

Haka kuma alkaluman NCDC sun nuna cewa an samu adadin da ba a taba samu ba na mafi yawan mutanen da suka kamu da cutar korona cikin jihohin Arewacin Najeriya a rana ɗaya.

KARANTA KUMA: Kusan duk wadanda cutar korona ta kama za su warke - NCDC

Sanarwar da taskar bayanai ta ma'aikatar lafiyar ta fitar da misalin karfe 11.55 a ranar Larabar da daddare, sun nuna cewa mutum 101 ne suka kamu da cutar korona a jihohi tara na Arewa ciki har da babban birnin kasar.

Ga jerin adadin mutanen da suka kamu da cutar a kowace daya daga cikin jihohi 35 na Najeriya da cutar ta bulla:

Lagos-931; Abuja-174; Kano-139; Ogun-50; Gombe-64; Osun-34; Katsina-40; Borno-59; Edo-37; Oyo-21; Kaduna-32; Bauchi-29; Akwa Ibom-12; Kwara-11; Sokoto-27; Ekiti-8; Ondo-8; Rivers-7; Delta-7; Taraba-8; Jigawa-7; Enugu-3; Niger-2; Abia-2; Zamfara-4; Benue-1; Anambra-1; Adamawa-2; Plateau-1; Imo-1; Bayelsa-2; Ebonyi-1; Kebbi-1; Nasarawa-1; Yobe-1.

Ga jerin adadin mutanen da cutar korona ta hallaka a jihohin Najeriya da cutar ta bulla:

Lagos (21), Abuja (3), Kano (3), Ogun (1), Kaduna (17), Akwa Ibom (1), Katsina (2), Sokoto (3), Edo (3), Borno (5), Ebonyi (1), Osun (2), Oyo (2), Ekiti (1), Delta (2), Rivers (2).

Sannan kuma ga jerin adadin mutanen da suka warke a jihohin Najeriya da cutar ta bulla:

Lagos (192), Abuja (36), Ogun (6), Kaduna (6), Bauchi (6) Akwa Ibom (9), Kwara (2), Anambra (1), Edo (9), Ondo (3), Enugu (2), Osun (18), Oyo (9), Ekiti (2), Delta (4), Rivers (2).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel