Corona: Gwamna ya umarci Ciyamomi su koma tsaron iyakokin garuruwansu don tare bakin haure

Corona: Gwamna ya umarci Ciyamomi su koma tsaron iyakokin garuruwansu don tare bakin haure

Gwamnan jahar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi ya umarci shuwagabannin kananan hukumomin jahar guda 17 da su koma su tare a bakin iyakokinsu domin yaki da yaduwar cutar Coronavirus.

Sakataren gwamnatin jahar, Simon Ortuanya ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, inda yace sun samu labarin bakin haure na cigaba da shiga jahar ta barauniyar hanya.

KU KARANTA: Mace mace a jahar Kano: Mutane 2 sun mutu dalilin cutar Coronavirus

Don haka gwamnan ya umarci Ciyamomi, kansiloli, masu mukaman gargajiya, yan banga, kungiyar matasa da sauran masu ruwa da tsaki a kan su fito su kare garuruwansu.

Corona: Gwamna ya umarci Ciyamomi su koma tsaron iyakokin garuruwansu don tare bakin haure

Gwamna Uguanyi
Source: UGC

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito kwanan nan aka sake samun bullar cutar Coronavirus a jahar Enugu bayan an sallami wasu mutum 2 da suka warke a baya.

Sakataren gwamnatin ya yi kira ga matafiya dake shirin shiga jahar da su dakatar da tafiyansu, idan kuma ba haka gwamnati za ta kwace duk motar da ta kama, kuma za ta hukunta su.

“Wannan halin tir da Allah wadai da wasu suke nunawa zai iya lalata kokarin da gwamnati take yi na yaki da cutar COVID19, za mu kai kaimi wajen gadin iyakokin garuruwanmu da daddare, musamman wadanda suke da iyaka da jahohin da suke da cutar.” Inji shi.

Sakataren ya kara da cewa duk wanda suka kama yana taimakon bakin haure wajen karya dokar shi ma zai dandana kudarsa, saboda za su kama shi, kuma su mika shi ga jami’an tsaro.

Shi ma kwamishinan kiwon lafiya na jahar, Farfesa Ikechukwu Obi ya bayyana cewa sun fara farautar mutanen da suka yi mu’amala da matar da ta sake kamuwa da cutar Corona a jahar.

Obi yace matar ta dawo jahar ne daga jahar Filato, don haka yayi kira ga duk wanda suka yi mu’amala da ita a kan su mika kansu ga hukuma domin a gwada su don tabbatar da lafiyarsu.

Daga karshe ya kara da cewa a yanzu Yansanda sun garkame gidan matar dake No 66 titin Nike, a unguwar Abakpa domin yi ma gidan feshin magunguna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel