Mace mace a jahar Kano: Mutane 2 sun mutu dalilin cutar Coronavirus

Mace mace a jahar Kano: Mutane 2 sun mutu dalilin cutar Coronavirus

Ma’aikatar kiwon lafiya ta gwamnatin jahar Kano ta sanar da karin mutuwar mutane 2 a sakamakon cutar COVID19 wanda aka fi sani da suna annobar Coronavirus.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito ma’aikatar ta bayyana haka ne cikin wani rubutu da ta wallafa a shafinta na kafar sadarwar zamani na Twitter, a ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu.

KU KARANTA: Mace mace a Kano: Wasu manyan mutane guda 3 sun sake mutuwa a jahar Kano

Hakan ya kawo adadin mutanen da suka kamu da cutar a jahar Kano zuwa 139 daga fara samun bullar cutar zuwa karfe 12:05 na daren Alhamis, 5 kuma suka mutu

Don haka ma’aikatar kiwon lafiya ta Kano take kira ga jama’an jahar su girmama dokar gwamnati na zaman gida domin kare yaduwar cutar a fadin jahar.

“Karin bayani a kan #COVID19KN a karfe 12:05 na daren 30 ga watan Afrilu, an samu karin mutane 24 da suka kamu da cutar, jimillan masu cutar a jahar sun kai 139, mutane 2 sun mutu. Don Allah a yi biyayya ga umarnin gwamnati na zaman gida don dakile cutar.” Inji ta.

Mace mace a jahar Kano: Mutane 2 sun mutu dalilin cutar Coronavirus

Hoto: Shafin Salihu Tanko Yakasai
Source: Facebook

Idan za’a tuna hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sanar da sabbin mutane 196 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, a yanzu mutane 1,728 ke da cutar a Najeriya.

Jahohin da aka samu sabbin masu cutar sun hada da Legas – 87, Kano – 24, Gombe - 18, Kaduna – 17, Abuja – 16, Katsina – 10, Sakkwato – 8, Edo – 7, Borno – 6, Yobe – 1, Ebonyi – 1 da Adamawa – 1.

Hukumar ta kara da cewa adadin wadanda aka sallama bayan sun warke daga cutar ya kai 307, sai kuma mutane 51 da suka mutu a sanadiyyar cutar.

A wani labari kuma, har yanzu ana cigaba da samun wadannan mace mace duk da matakin da gwamnatin jahar da ta tarayya suka ce suna dauka game da lamarin.

Daily Trust ta ruwaito a ranar Laraba, 29 ga watan Afrilu ma an sake samun ire iren mace macen nan a jahar Kano, inda wasu manyan mutane guda uku suka mutu a rana daya.

Wadannan mutane uku da suka mutu sun hada da Alhaji Salisu Ado, Alhaji Aminu Yahaya da kuma Alhaji Muhammad Aliyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel