A rana ɗaya Coronavirus ta harbi mutane 101 a Arewacin Najeriya

A rana ɗaya Coronavirus ta harbi mutane 101 a Arewacin Najeriya

Hukumar yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC, ta ce a ranar Laraba 29 ga watan Afrilu, an samu adadi mafi yawa na mutanen da suka taba kamuwa da cutar korona a Arewacin kasar.

Alkaluman NCDC sun nuna cewa an samu adadin da ba a taba samu ba na mafi yawan mutanen da suka kamu da cutar korona cikin jihohin Arewacin Najeriya a rana ɗaya.

Sanarwar da taskar bayanai ta NCDC ta fitar da misalin karfe 11.55 a ranar Laraba da daddare, sun nuna cewa mutum 101 ne suka kamu da cutar korona a jihohi goma ciki har da babban birnin kasar.

Kididdigar alkaluman ta nuna jihar Kano ce ke da mafi yawan kaso da mutum 24, sai kuma Gombe mai mutum 18 yayin da Kaduna aka samu mutum 17.

A birnin tarayya Abuja an samu mutum 16 da cutar ta harba, inda Katsina ta samu mutum 10, yayin da birnin Shehu wato Sokoto aka samu mutum 8.

Jihar Borno ta biyo baya da mutum 6 yayin da jihar Yobe wadda aka samu bullar cutar karon farko ita mutum daya ya kamu.

Shugaban NCDC na Najeriya; Chikwe Ihekweazu
Shugaban NCDC na Najeriya; Chikwe Ihekweazu
Asali: Facebook

Likafar cutar korona na ci gaba yayin da alkaluman masu kamuwa da cutar ke kara hauhawa cikin dan kankanin lokacin a jihohi Kano da Borno da Gombe da kuma Katsina.

A ranar Juma'a 20 ga watan Maris ne dai aka fara samun bullar cutar a yankin Arewacin Najeriya, lokacin da dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Muhammad Atiku ya kamu da ita bayan ya dawo kasar a garin Abuja.

A kwanaki 40, alkaluman hukumar NCDC sun tabbatar da cewa mutum 603 ne suka kamu da cutar korona a jihohi 19 na Arewacin Najeriya ciki har da garin Abuja.

Wannan adadi na mutanen da cutar ta harba a Arewa shi ne kimanin kashi 40% na masu fama da annobar a fadin Najeriya.

Har yanzu, jihar Kogi ce kadai ba a samu bullar cutar ba cikin dukkanin jihohin yankin Arewacin Najeriya.

A jihar Bauchi ne aka samu bullar cutar koron farko a Arewacin Najeriya baya ga birnin Abuja. Gwamnan jihar Bala Muhammad shi ne wanda ya fara kamuwa a ranar Talata, 24 ga watan Maris.

Mun ji cewa ma'aikatar lafiyar ta Kano da ke Arewa maso Yamma a Najeriya, ta ce ya zuwa adadin mutanen da cutar korona ta harba a jihar sun kai 139 tun bayan da ta fara bulla a jihar.

Jadawalin jihohin da cutar mai sanya sarkewar numfashi ta bulla ya nuna Kano ce ta uku a yawan masu fama da cutar bayan Legas mai mutum 931 da birnin Abuja inda ake da mutane 174.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng