Ana takaddama kan kama matashin da ya yi wa Annabi batanci

Ana takaddama kan kama matashin da ya yi wa Annabi batanci

Wasu yan Najeriya a ranar Laraba sun bayyana rashin jin dadin su game da kama wani mulhidi, Mubarak Bala da Rundunar Yan sandan jihar Kaduna ta yi saboda rubutu da ya wallafa a shafin Facebook inda aka ce ya yi wa Annabi Muhammad batanci.

An kama Bala ne a gidansa da ke Kaduna bayan wasu lauyoyi sunyi wa Kwamishinan Yan sandan Kano korafi tare da neman a gurfanar da shi a kotu saboda kalaman da ya wallafa “na tunzura mutane.”

Korafin lauyoyin, mai dauke da sa hannun S.S Umar ya bayyana cewa, "mun kawo korafi ne a kan wani mai suna Mubarak Bala dan unguwar Karkasara a Kano.

"An haifi Mubarak a gidan Musulunci amma saboda wasu dalilai na kashin kansa sai ya zabi ya bar addinin, ya zama marar addini, a 2014. Tun da ya bar addini ya ke wallafa sakonnin da basa yi wa Musulmai dadi a shafinsa na 'Facebook'.

Ana takaddama kan kama matashin da ya yi wa Annabi batanci
Ana takaddama kan kama matashin da ya yi wa Annabi batanci
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: COVID-19: El-Rufai ya bada sharudda 3 na sassauta doka a jihar Kaduna

Kazalika, wata kungiya mai suna Change.org ta gabatar da korafi na neman a rufe shafin Facebook na Mubarak Bala. A safiyar ranar Laraba, mutum 16,942 sun rattaba hannu kan takardan korafin na neman a rufe shafin na Bala.

Ana sa ran za a gurfanar da Bala a gaban kotu kan laifin batanci ga addinin musulunci wanda laifi ne da ya ci karo da dokar Sharia ta jihar.

Wasu masu amfani da dandalin sada zumunta da suka yi rubutu a shafin Punch sun soki kama shi.

Wani mai suna Mattos ya ce, "Yan sanda, ba ku da aiki. Barayi da masu garkuwa da mutane suna cin karensu ba babbaka amma kuna bata lokacin ku a kan batun addini."

Tsunami1earthquake ya ce, "Amma wannan mutum ya yi wa Kiristanci batanci; mene yasa kiristoci ba su harzuka ba? Abokai na, kowa ya yi addininsa kawai, kada ka kula abinda wani ke fadi a kan ka. Ka bari Allah ya yi hukunci. Fakat."

Akano ya ce, "Toh fa, dukkan addinan biyu fa kawo mana su kasar mu, Najeriya, aka yi amma kullum muna ta hayaniya kamar dama addinan na mu ne."

OgbuefiIdris ya ce, "Mutane su dena bata lokacin su domin babu wani Annabi da ya yi korafi. Wadanda suke rubuta korafin ba sune Annabi Muhammadu ba. Ko shi Annabi TB Joishua bai yi korafi ba. Saboda haka mutane suyi abinda ke gaban su kawai."

Da aka tuntube shi, Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige ya ce, "Ba zan iya cewa komai ba game da laifinsa ko dalilin da yasa aka kama shi. An dai sanar da mu ne kawai mu kama shi. Rundunar Yan sandan Kano ce za ta iya bayar da bayani."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel