Kusan duk wadanda cutar korona ta kama za su warke - NCDC

Kusan duk wadanda cutar korona ta kama za su warke - NCDC

- Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa NCDC ta tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa akasarin masu cutar korona a kasar za su murmure

- A kiyasin shugaban NCDC, Dr Chikwe Ihekweazu, ya ce kashi 95 zuwa 98 na marassa lafiyar za su warke ba tare da shan wani magani ba

- A cewarsa, dalilin kadai da ya sanya ake kebance masu cutar a killace shi ne hana yaduwarta

Shugaban NCDC, Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a Najeriya, Dr Chikwe Ihekweazu, ya ce kaso 95 zuwa 98 na masu dauke da cutar korona a kasar za su warke garau.

Dr Chikwe ya ce kusan dukkanin wadanda cutar korona ta harba a kasar nan za su murmure ba tare shan wani magani ba ko samun kulawa ta kwararrun lafiya ba.

Furucin Dr Chikwe ya zo ne cikin birnin Abuja a ranar Laraba, 29 ga watan Afrilun, yayin ganawa da kwamitin kar ta kwana da fadar shugaban kasa ta kafa a kan cutar korona.

A cewarsa, ba wani dalili ya sanya ake kebance masu cutar a killace ba face hana yaduwarta kadai. Amma cutar ba wata tsiya bace.

A kalamansa: "Alamomin cutar korona ba su bayyana ba a jikin mafi akasarin wadanda ta harba kuma za su murmure ba da dade wa ba."

Shugaban NCDC; Dr. Chikwe Ihekweazu
Shugaban NCDC; Dr. Chikwe Ihekweazu
Asali: UGC

"Dalilin kadai da ya sanya muke kebance wadanda cutar ta harba a cibiyoyyin killacewa bai wuce fafutikar mu ta hana yaduwarta ba gwargwadon iko."

Sai dai ya ce "kashi 5 zuwa 15 cikin 100 bisa la'akari da inda suke, za su kuma da tsananin rashin lafiya ta cutar kuma wasun su za su mace."

KARANTA KUMA: Faloli 6 na azumin watan Ramalana

A halin yanzu akwai jihohi 36 da cutar ta bulla ciki har da babban birnin kasar nan, sai dai shugaban na NCDC ya yi gargadin cewa babu jihar da ta tsira daga hadarin barkewar cutar.

Ya ce: “Don haka yin shige-da-fice a tsakanin jihohi zai kara jefa kasar nan cikin hadarin gaske na ci gaba da yaduwar wannan annoba.

"Matakan da muka dauka na dakile yaduwar cutar sun yi daidai da shawarwarin hukumomin lafiya na duniya."

"Kuma wannan fada ne na mu duka da sai kowa ya tashi tsaye wajen ganin cutar ba ta yi mana illa ba sosai."

"Don haka, duk matakan da za mu dauka, dole ne samu hada kai yayin aiwatar da su baki daya, walau mun kasance a Arewa, Kudu, Gabas ko Yammacin kasar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel