Rahoton Oronsanye: Buhari ya bayar da umurnin soke wasu ma'aikatu da hukumomin gwamnati

Rahoton Oronsanye: Buhari ya bayar da umurnin soke wasu ma'aikatu da hukumomin gwamnati

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da aiwatar da shawarwarin da kwamitin shugaban kasa a kan yi wa hukumomi da ma'aikatun gwamnatin tarayya garambawul a lokacin mulkin Goodluck Jonathan ta bayar.

Rahoton da ake yi wa lakabi da rahoton Oransaye mai shafi 800 ya bayar da shawarar soke wasu hukumomi tare da gwamutsa wasu ma'aikatun gwamnati 102.

Ministan Kudi, Zainab Ahmed, a ranar Laraba a Channels TV ta ce Shugaban kasa ya amince da aiwatar da shawarwarin da ke rahoton kuma an mika rahoton ga shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya.

Rahoton Oronsanye: Buhari ya bayar da umurnin soke wasu maaitaku da gwamutsa wasu
Rahoton Oronsanye: Buhari ya bayar da umurnin soke wasu maaitaku da gwamutsa wasu
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: COVID-19: El-Rufai ya bada sharudda 3 na sassauta doka a jihar Kaduna

Ahmed ta ce, "Shugaban kasa ya amince gwamnatinsa ta aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahoton Oransanye."

"Kwamitin ta yi nazarin hukumomin gwamnati ta kuma bayar da shawarwarin rage adadin su wanda hakan na nufin za a gwamutsa wasu hukumomi da ma'aikatun.

"Wannan rahoton ya dade a ajiye amma ba a aiwatar da shawarwarin da ke cikin sa ba amma yanzu shugaban kasa ya amince da shi kuma mun aike da sakon shugaban kasar ga ofishoshin da za su dauki mataki a kai suna ofishin sakataren gwamnatin tarayya da na shugaban ma'aikatan tarayya."

Tsohon shugaban ma'aiktan gwamnatin tarayya, Stephen Oransaye ne ya jagoranci kwamitin da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa domin gano hanyoyin inganta aikin gwamnati.

A lokacin, kwamitin mai mambobi bakwai ta ce "kafa hukumomi, ma'aikatu da cibiyoyi na bukatar kudi a mutane da za suyi aiki a wuraren" kuma ta bada shawarar gwamnati ta mayar da hankali wurin inganta kalilan da ake da su su inganta ayyukansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel