Annobar Coronavirus: Yan bursuna sun yi bore a Delta, 2 sun tsere, an bindige guda 5

Annobar Coronavirus: Yan bursuna sun yi bore a Delta, 2 sun tsere, an bindige guda 5

Wasu mazauna gidan yari guda biyu sun tsere daga kurkukun garin Sapele na jahar Delta bayan barkewar wani kazamin rikici da yayi sanadiyyar harbin mutane 5.

Daily Trust ta ruwaito wata matajiya mai karfi ta shaida mata cewa mutanen biyu sun tsere ne ta tagogin sashin dakunan mata dake kurkukun, kuma har yanzu ba’a san inda suka shiga ba.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus ta kashe mutane 3 a jahar Sakkwato – Gwamna Tambuwal

Rikicin ya samo asali ne bayan gwamnatin jahar ta yiwa mazauna kurkukun su 150 afuwa a wani mataki na rage cunkoson kurkukun don kare yaduwar annobar Coronavirus.

Hakan ne yasa wasu fursononi yin bore tare da zargin gwamnatin jahar da nuna son kai wajen zaban wadanda suka ci gajiyar afuwar, daga nan sai fada ya kaure.

Ana haka ne sai suka fara yunkurin tserewa daga kurkukun, a nan ne jami’ai suka bindige mutane 5 wanda a yanzu suna samun kulawa sakamakon munanan rauni da suka ji.

Annobar Coronavirus: Yan bursuna sun yi bore a Delta, 2 sun tsere, an bindige guda 5
Annobar Coronavirus: Yan bursuna sun yi bore a Delta, 2 sun tsere, an bindige guda 5
Asali: Facebook

Shi ma wani jami’in tsaro ya bayyana cewa: “Fursunonin basu samu bayanin da ya kamata ba, sun dauka afuwar COVID19 kowa za ta shafa, don haka suke bukatar a yi ma kowa afuwan, ta yaya za’a saki kowa? Bayan akwai masu kisan mutane, yan fyade da sauran miyagu a cikinsu?”

Kakaakin Yansandan jahar, Onome, ya tabbatar da yamutsin: “Tabbas ya faru, mutane 2 sun tsere daga cikinsu, an kuma bindige guda biyar yayin da suka yi kokarin tserewa, a yanzu suna asibiti.”

Shi ma kakaakin hukumar gidajen yari ta kasa reshen jahar Delta, Uche Mgbakor ta tabbatar da aukuwar lamarin, amma ta ce tuni sun fara farautar wadanda suka tseren.

“Tuni hukuma ta aika da kwararrun jami’ai masu iya bincike cikin sirri domin su gano inda mutanen suka shiga, tare da kama su domin mayar da su kurkukun da suka fito.” Inji ta.

A wani labari kuma, Kwamishinan Yansandan jahar Kaduna, Umar Musa Muri ya ce sun kama Malaman addinai guda 48 sakamakon karya dokar ta baci da gwamnati ta sanya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng