Mace mace a Kano: Wasu manyan mutane guda 3 sun sake mutuwa a jahar Kano

Mace mace a Kano: Wasu manyan mutane guda 3 sun sake mutuwa a jahar Kano

Tun a makon da ta gabata ne al’ummar Kano suka shiga cikin halin fargabar bayan samun mace macen mutane da dama a jahar cikin yan kwanaki kadan ba tare da sanin sababi ba.

Sai dai har yanzu tsuguni bata kare ba, sakamakon ana cigaba da samun wadannan mace mace duk da matakin da gwamnatin jahar da ta tarayya suka ce suna dauka game da lamarin.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus ta kashe mutane 3 a jahar Sakkwato – Gwamna Tambuwal

Daily Trust ta ruwaito a ranar Laraba, 29 ga watan Afrilu ma an sake samun ire iren mace macen nan a jahar Kano, inda wasu manyan mutane guda uku suka mutu a rana daya.

Wadannan mutane uku da suka mutu sun hada da Alhaji Salisu Ado, Alhaji Aminu Yahaya da kuma Alhaji Muhammad Aliyu.

Mace mace a Kano: Wasu manyan mutane guda 3 sun sake mutuwa a jahar Kano

Mariyagi Salisu Ado
Source: Facebook

Marigayi Salisu Ado dan asalin garin Daura ne, amma mazaunin Kano, tsohon daraktan kudi na asibitin kashi dake Kano, haka zalika tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar Daura.

Salisu Ado ya rasu ne da sanyin safiyar Laraba bayan fama da rashin lafiya da ta danganci wahalar shakar numfashi, duk kokarin da likitoci suka yi na ceton shi ya ci tura.

Alhaji Aminu Yahaya kuwa tsohon shugaban wata hukumar gwamnatin jahar Kano, kuma ya taba zama kwamishinan ilimi a jahar Kano.

Yayin da Alhaji Muhammad Aliyu shi ne tsohon babban sakataren hukumar ilimi ta jahar Kano, kuma an gudanar da jana’izar sa ne a rukunin gidaje a GATC dake Kabuga, jahar Kano.

Tun farkon wannan lamari, al’ummar jahar Kano da wasu masana kiwon lafiya sun danganta mace macen da annobar Coronavirus, musamman duba da alamominta.

Amma gwamnatin Kano ta ce ta gano dalilan da suka kawo mace macen, inda ta danganta su ga cututtukan hawan jini, ciwon siga, sankarau da kuma cutar zazzabib cizon sauro.

Gwamnatin ta ce ta gano haka ne bayan sun gudanar da cikakken bincike game da mace mace, don haka yace mace macen basu da alaka da Coronavirus, saboda haka kada jama’a su firgita.

A wani labarin kuma, an sake tsintar gawar wani mutumi a karkashin gadar Kwankwasiyya dake kofar Nassarawa a ranar Talata, 28 ga watan Afrilu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel