Kaduna ta samu kaso mafi tsoka cikin N43.4bn da gwamnati ta raba wa jihohi

Kaduna ta samu kaso mafi tsoka cikin N43.4bn da gwamnati ta raba wa jihohi

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta raba wa jihohi 24 a kasar Kudi Naira Biliyan 43,416 a matsayin tallafi cikin kudin da Bankin Duniya ta bawa jihohi bisa laakari da jajircewa da suke yi wurin yaki da cutar.

Ministan Kudi, Zainab Ahmed cikin sanarwar da ta fitar ya nuna cewa jihohin da suka amfana da tallafin sun hada da Abia, Adamawa, Bauchi, Benue, Delta, Edo, Ekiti, Enugu, Gombe.

Sauran sune Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Niger, Ondo, Ogun, Oyo, Osun, Sokoto, Taraba da Yobe states.

A cewar sanarwar mai dauke da saka hannun Direktan yada labarai na maaikatar, Hassan Dodo, kawo yanzu an raba wa jihohi 24 jumullar kudi N43,416,000,000.00 wanda ya yi dai dai da Dalla Miliyan 120.6.

Kaduna ta samu kaso mafi tsoka cikin N43.4bn da gwamnati ta raba wa jihohi
Kaduna ta samu kaso mafi tsoka cikin N43.4bn da gwamnati ta raba wa jihohi
Asali: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)

Jihar Kaduna ce kan gaba wurin cika kaidojin samun tallafin hakan ya sa ta fi samun kaso mafi tsoka na N3,960,000,000.00.

Jihohin Katsina da Benue ne suka samu kaso mafi karanci na N540,000,000.00 kowannen su.

Ministan ya yi bayanin cewa an yi rabon tallafin ne bisa laakari da kiyaye kaidojin samun tallafin da ake gudanarwa a duk shekara.

A cewar ta, Ofishin Audita Janar na kasa tare da hadin gwiwar wani kamfani daga kasar Birtaniya da SFTAS ne suka gudanar da kididigan tantance cancantar jihohin.

Mrs Ahmed ta ce gwamnatin tarayya ta kafa tsarin na SFTAS ne domin bawa jihohi tallafi bisa laakari da irin kwazo da jajircewarsu.

MInistan ta ce duk jihar da ta ke son amfani da tallafin sai ta rika wallafa kasafin kudin ta a shafin yanar gizo a duk shekara da wasu bayanan da zai nuna yadda jihar ke kashe kudadenta.

Jihohin da ba su samu tallafn ba saboda rashin cika kaidojin sun hada da Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Borno, Cross River, Ebonyi, Imo, Lagos, Nasarawa, Plateau, Rivers da Zamfara States.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel