Coronavirus: Yansanda sun kama Malaman addini guda 48 a jahar Kaduna

Coronavirus: Yansanda sun kama Malaman addini guda 48 a jahar Kaduna

Kwamishinan Yansandan jahar Kaduna, Umar Musa Muri ya bayyana cewa sun ta kama Malaman addinai guda 48 sakamakon karya dokar ta baci da gwamnati ta sanya.

Daily Trust ta ruwaito kwamishinan yace baya ga Malamai 48, rundunar su ta kama wasu mutane dake gudanar da wuraren da ake sayar da barasa a jahar, duk a kan wannan laifi.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus ta kashe mutane 3 a jahar Sakkwato – Gwamna Tambuwal

Kwamishinan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Laraba, 29 ga watan Afrilu yayin da yake holen mutanen a babban ofishin rundunar Yansandan jahar.

Kwamishina Muri ya kara da cewa sun kama mutane 986 da laifin yi ma dokar karan tsaye, tun daga ranar 26 ga watan Maris, kuma sun gurfanar da su gaban kotu don fuskantar hukunci.

Coronavirus: Yansanda sun kama Malaman addini guda 48 a jahar Kaduna

Coronavirus: Yansanda sun kama Malaman addini guda 48 a jahar Kaduna
Source: Twitter

“Mun gurfanar da duk wadanda muka kama da laifin yi ma dokar hana shige da fice karan tsaye zuwa gaban kotu, adadinsu ya kai 986, 48 daga ciki malaman addinai ne, sai kuma masu cinikin barasa.

“Haka zalika mun kama mutane 91 da aikata laifuka daban daban a jahar da suka hada da yan bindiga, masu garkuwa da mutane, masu laifin kisan kai, yan fyade, barayi da sauransu.” Inji shi.

A hannu guda kuma, kwamishina Muri yace sun kaddamar da wani samame tare da hadin gwiwar rundunar Sojin sama a sansanin yan bindiga inda suka kashe miyagun mutane 40.

Muri yace sun kai wannan samame ne a ranar 21 ga watan Feburairu a sansanonin yan bindiga guda hudu, kamar yadda suka yi a ranar 17 ga watan Maris inda suka kashe yan bindiga 60.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana mutuwar wasu mutane 3 daga cikin mutane 10 dake dauke da cutar Coronavirus a jahar.

Sanarwar ta ce: “Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jahar Sakkwato ya sanar da mutuwar mutane 3 a sanadiyyar cutar COVID19, duka mamatan uku suna da tattare da wasu cututtuka dake damunsu kamar ciwon siga, ciwon asma da kuma hawan jini.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel