Da duminsa: Allah y yiwa tsohon gwamnan jihar Borno rasuwa

Da duminsa: Allah y yiwa tsohon gwamnan jihar Borno rasuwa

- Tsohon gwamnan jihar Borno, Alhaji Muhammad Goni, ya kwanta dama

- Goni ya rasu ne a ranar Laraba, 29 ga Afrilu, 2020 bayan gajeruwar rashin lafiya

- Marigayin ya mulki jihar Borno tsakanin 1979 da 1983

Rahotanni daga jihar Borno sun tabbatar da rasuwar tsohon gwamnan jihar, Alhaji Muhammad Goni, ya rigamu gidan gaskiya.

Mun samu labarin cewa tsohon gwamnan ya rasu ne ranar Laraba, 29 ga Afrilu, 2020 bayan gajeruwar rashin lafiya da yayi fama da shi.

Legit ta tattaro cewa Goni ya kasance tsohon ma'aikacin gwamnati wanda ya mulki tsohuwar jihar Borno tsakanin shekarar 1979 zuwa 1983.

An haifi marigayin ne a shekarar 1942 a Kareto, karamar hukumar Mobbar na jihar Borno.

Ya yi karatunsa a makarantar Maiduguri Middle School (1953–55), Borno Provincial Secondary School (1956–61), Provincial Secondary School, Kano (1962–63) sai kuma jami'ar Ahmadu Bello University, Zaria (1964–87).

Da duminsa: Allah y yiwa tsohon gwamnan jihar Borno rasuwa
Da duminsa: Allah y yiwa tsohon gwamnan jihar Borno rasuwa
Asali: UGC

KU KARANTA: Gangancin Jami’an tsaro ya sa cutar COVID-19 ta ke yaduwa sosai a Ondo – Akeredolu

Mutuwar Goni ta biyo bayan mutuwar Shehun Bama, mai martaba Kyari Ibn Umar El-Kanemi.

Alhaji Kyari Ibn Umar El-Kanemi ya rasu a ranar Litinin, 27 ga watan Afrilu, ranar azumin Ramadana na 4.

Daily Trust ta ruwaito gwamnatin jahar Borno ce ta tabbatar da mutuwar basaraken mai daraja na daya a jerin masarautun jahar Borno, inda tace ya rasu ne a wani asibiti dake Maiduguri.

Marigayi Kyari shi ne Shehun tsohuwa masarautar Dikwa na 7, wanda ya hada da kananan hukumomin Bama, Dikwa, Ngala da Kala-Balge.

A shekarar 2010 ne gwamnatin jahar Borno ta raba masarautar gida biyu zuwa Bama da Dikwa, kuma ta baiwa kowannensu Sarki mai daraja na daya.

Kwamishinan watsa labaru da al’adun gargajiya na jahar, Babakura Abba Jato ne ya sanar da rasuwar basaraken yayin da yake jawabi game da halin da ake ciki a jahar game da COVID-19.

Jato ya ce Shehu ya dade yana fama da rashin lafiya a sanadiyyar tsufa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel