Rikicin addini ya barke a tsakanin 'yan Najeriya da ke kasar Kamaru

Rikicin addini ya barke a tsakanin 'yan Najeriya da ke kasar Kamaru

- Rikici da hargitsi ya barke tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kiristanci a sansanin 'yan gudun hijirar Najeriya da ke Kamaru

- Sakamakon wannan rikicin, an samu mutane da dama da suka samu raunika miyagu a sansanin Minawao

- Kamar yadda wata majiya ta bayyana, an yi fadan ne tsakanin kananan yara 'yan asalin jihar Borno ta Najeriya

Rikicin addini ya barke tsakanin mabiya addinin Musulunci da na Kiristanci a sansanin 'yan gudun hijirar Najeriya da ke Kamaru.

Lamarin ya faru ne a sansanin Minawao a ranar Laraba.

Wannan lamarin ne ya kai ga rushe gidaje da kona wasu sassa biyu na masu adawa da juna, ballantana na mazauna shiyya ta biyu da ta uku na sansanin.

Hakazalika, sun ji wa juna miyagun rauni da makamai. Amma kuma jami'an tsaro sun shiga tsakaninsu don kawo lafawar rikicin.

Rikicin addini ya barke a tsakanin 'yan Najeriya da ke kasar Kamaru

Rikicin addini ya barke a tsakanin 'yan Najeriya da ke kasar Kamaru
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Sanannun mutum 11 da suka rasu a Kano a cikin kwana 4

Wakilin BBC a Kamaru ya ce akwai alamun da ke nuna cewa dukkan bangarorin 'yan asalin jihar Borno ne kuma sun fito ne daga kananan hukumomin Goza da Bama.

Rikicin ya tsinke ne a tsakanin yara biyu kanana na Musulmi da Kirista. Lamarin har ya kai ga kaurewar dambe.

Bayan mahaifin Musulmin ya raba fadan ne sai mahaifin dayan yaron ya ce ba a yi wa yaronsa adalci ba.

Iyayen yaran sun ci gaba da husuma tsakaninsu inda daga nan labarin ya shiga unguwanni sai rikicin ya zama na bambancin addini.

A wani labari na daban, ma'aikatan lafiya na kasar Jamus sun wallafa hotunansu tsirara don janyo hankulan gwamnati a kan shiga sahun gaba da suke wajen yakar annobar COVID-19 amma babu kayan kariya.

Kamar yadda jaridar The Nation Online ta ruwaito, kungiyar mai suna Blanke Bedenken ta kafu ne don kira ga ministan lafiya na kasar Jamus a kan halin da suke ciki na wata da watanni.

Sun ce, "idan kayayyakin kariya suka kare mana, haka muke komawa. Wannan ne halin da muke ciki a yanzu da bamu da kayayyakin kariya, tamkar tsirara muke."

Arztezeitung ta wallafa: "Wannan tsiraicin na nuna yadda cutar za ta iya kama mu kenan ba tare da kariya ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel