Yanzu-yanzu: Gobara ta lamushe shaguna masu yawa a garin Kaduna
A kalla shaguna 20 wadanda suka hada da wurin siyar da magani ne suka babbake a jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne wurin karfe 7 na yamma a wurin Constitution road da ke babban birnin jihar.
Har a halin yanzu ba a san musabbabin gobarar ba, gidan talabijin din Channels ne ya wallafa.
A yayin da ake fitar da wannan rahoton, jami'an hukumar kwana-kwana da sauran masu taimakon gaggawa duk basu isa wurin ba.
Amma kuma, mazauna yankin tare da masu wucewa ne ke kokarin kashe gobarar.
Hakazalika, babu daya daga cikin masu shagunan da ke kusa saboda dokar hana zirga-zirgar da gwamnatin jihar ta saka don yaki da cutar COVID-19.

Asali: Twitter
KU KARANTA: COVID-19: Ganduje ya bayyana yadda cutar ke yaduwa a jihar Kano
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng