Da duminsa: Bankuna za su iya budewa a Legas, Abuja da Ogun
Kwamitin kar ta kwanan fadar shugaban kasa kan yaki da cutar COVID-19 ta ce rassan bankuna a jihar Legas, jihar Ogun da birnin tarayya Abuja za su iya fara budewa daga ranar Litnin, 4 ga Mayu.
Shugaban kwamitin, Sani Aliyu, ya ce za'a amince bankunan su bude daga karfe 8 na safe zuwa 2 na rana.
Sani ya kara da cewa ofisoshin ma'aikatun gwamnatin tarayya da kamfanoni da masana'antun masu kere-kere zasu iya budewa.
Zaku tuna cewa tun ranar 29 ga Maris, shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin rufe dukkan masana'antu da ofisoshin gwamnati domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.
Yace:"Za'a amince ma'aikatan gwamnati su koma bakin aiki daga ranar 4 ga Mayu amma ba dukkan ranakun mako za'a amince su fita ba kuma ba dukkan ma'aikata ba saboda rage cinkoso a ofisoshin."
"Za'a amince bakuna su bude amma za'a rage awannin budewa zuwa karfe 8 na safe zuwa 2 na rana tare da biyayya da lura da dukkan dokokin kare kai da na ambata a baya."
"Hakazalika za'a amince masu gina tituna masu muhimmanci su cigaba da aiki amma sai gwamnatocin jihohi sun basu dama."

Asali: UGC
KU KARANTA: Annobar covid-19 ta harbi sabbin mutane 195 a Najeriya, 38 a Kano
Gwamnatin jihar Legas ta sanar da sallamar majinyata 49 dake kwance a cibiyoyin killacewanta na muguwar cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus (COVID19).
Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana hakan ne a hirar da yakeyi yanzu haka da manema labarai a unguwar Marina ta jihar.
Ya ce 48 yan Najeriya ne yayinda 1 bature.
Hakazalika Ma'aikatar kiwon lafiyar jihar ta bayyana hakan a jawabin da ta sake a shafin na Tuwita inda tace mutanen 49 sun hada maza 21 da mata 28.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng