Yanzu-yanzu: An sallami mutane 49 da suka warke daga Coronavirus yau a Legas kadai

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 49 da suka warke daga Coronavirus yau a Legas kadai

Gwamnatin jihar Legas ta sanar da sallamar majinyata 49 dake kwance a cibiyoyin killacewanta na muguwar cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus (COVID19).

Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana hakan ne a hirar da yakeyi yanzu haka da manema labarai a unguwar Marina ta jihar.

Ya ce 48 yan Najeriya ne yayinda 1 bature.

Hakazalika Ma'aikatar kiwon lafiyar jihar ta bayyana hakan a jawabin da ta sake a shafin na Tuwita inda tace mutanen 49 sun hada maza 21 da mata 28.

Jawabin tace: "Mata 28 da maza 21 hade da dan kasar Greece aka sallama daga cibiyoyin killacewanmu dake Yaba da Onikan kuma tuni an hadasu da iyalansu."

"Marasa lafiyan; 18 daga asibitin Yaba da 31 daga cibiyar Onikan sun murmure gaba daya bayan gwaji biyu daban-daban sun tabbatar da cewa sun barranta dake cutar."

"Kari da wannan, adadin wadanda akayi jinya kuma aka sallama a jihar Legas ya kai 187."

KU KARANTA: Annobar covid-19 ta harbi sabbin mutane 195 a Najeriya, 38 a Kano

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 49 da suka warke daga Coronavirus yau a Legas kadai

Yanzu-yanzu: An sallami mutane 49 a Legas
Source: Depositphotos

Kwamitin kar ta kwanan fadar shugaban kasa kan yaki da cutar COVID-19 ta ce rassan bankuna a jihar Legas, jihar Ogun da birnin tarayya Abuja za su iya fara budewa daga ranar Litnin, 4 ga Mayu.

Shugaban kwamitin, Sani Aliyu, ya ce za'a amince bankunan su bude daga karfe 8 na safe zuwa 2 na rana.

Sani ya kara da cewa ofisoshin ma'aikatun gwamnatin tarayya da kamfanoni da masana'antun masu kere-kere zasu iya budewa.

Zaku tuna cewa tun ranar 29 ga Maris, shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin rufe dukkan masana'antu da ofisoshin gwamnati domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel