An kama wani kasurgumin dan bindiga a Legas

An kama wani kasurgumin dan bindiga a Legas

Yan sanda sun kama wani gaggararren dan bindiga da ya dade yana adabar mutanen unguwanin Idimu da Ejigbo a Legas kamar yadda Linda Ikeji Blog ta ruwaito.

An kama Wahab Lawal ne da aka fi sani da Lordstime tare da wani dan kungiyarsa, Seun Adeniyi. Su biyu ne suka jagoranci wani hari da aka kai a Idimu kwanakin baya inda wani ya rasa ransa kamar yadda PM Express ta ruwaito.

Bayan harin, Lawal ya tsere kuma ya buya. Amma yan sandan Ejigbo karkashin jagorancin DPO, CSP Olabisi Okuwobi sun kama shi a Mafor kuma suka mika shi ga yan sandan Idimu.

A lokacin da aka kama shi, yan sandan sun kwato wani gatari na musamman da ake zargin shi Lawal ke amfani da shi wurin kashe mutanen da ya ke yi wa fashi. Tuni dai an mika wa DPO na Idimu, CSP Adora Dimaka makamin.

An kama wani kasurgumin dan bindiga a Legas
An kama wani kasurgumin dan bindiga a Legas
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)

Da aka fara bincike, An ce Lawal ya tona asirin wani malaminsa kuma mai gidansa mai suna Emir. Ya kuma ambaci sunan wani dan kungiyar kuma tuni an kamo su suna tsare a caji ofis na Idimu.

Kama wadanda ake zargin ya janyo murna da farin ciki a unguwannin Idimu da Ejigbo saboda mutanen unguwannin sun dade suna fama da yan kungiyar kafin a kama su.

A halin yanzu an mika su zuwa sashin binciken manyan laifuka SCIID Panti da ke Yaba a Legas domin cigaba da bincike.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, DSP Bala Elkana ya tabbatar da kama wadanda ake zargin da ma wasu daban a wasu unguwanni.

Ya yi alkawarin sai bayar da cikakken bayani game da muggan ayyukan da suke aikatawa a jihar nan gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel