Jerin sunaye: Buhari ya nada mambobin hukumar FCC guda 38
Shugaba Muhammadu Buhari ya nada mutane 38 a matsayin mambobin Hukumar tabbatar da daidaito a daukan ma'aikatan tarayya (FCC).
A cikin wasikar da ya aike wa Majalisar Dattawa a ranar Talata, Shugaban kasar ya bukaci majalisar ta amince da nadin.
Shugaba Buhari ya yi hakan ne kamar yadda sashi na 154 (1) na kundin tsarin mulki ta tanada.
Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan ya karanto wasikar a zauren majalisar a ranar Talata.
Wasikar ta ce, "Kamar yadda sashi na 154 (1) na kudin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima ta tanada, Na rubuto domin neman amincewar Majalisar Dattijai game da nadin mutum 38 a matsayin shugaba da mambobin hukumar tabbatar da daidaito a daukan ma'aikatan tarayya."
Wannan na zuwa ne kimanin watanni biyu bayan Majalisar ta bukaci Buhari ya zabi mambobin Hukumar ta FCC.
Tun kafa hukumar, kwamishina daya tak gare ta kamar yadda doka ta tanada. Abdullahi Halidu Shinkafi, kwamishinan kwara daya tak ya yi ritaya.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: COVID-19: Sabon salon sallar jam'i a kasashen duniya (Hotuna)
Ga sabbin mambobin hukumar da shugaban kasar ya nada:
1. Muheeba Dankaka - Shugaba
Mambobi
2. Henry Ogbulogo
3. Salihu Bella
4. Obonganwan Dorah Ebong
5. lbeabuchi Uche
6. Mohammad Tijjani
7. Tonya G. Okio
8. Silas Mfa Madkpah
9. Abba Ali Monguno
10.Nsor Atamgba
11. Alims Agoda
12. Tobias Chukwuemeka
12. lmuetinyan Festus,
14. Sesan Fatoba
15. Ginika Florence Tor
16. Hamza Mohammad
17. Diogu Uche
18. Lawan Ya’u Roni
19. Hadlza Usman Muazu
20. Muhammad Awwal Na’lya
21. Lawal Garba
22. Abubakar Atiku Bunu
23. Idris Bello
24. Daniel James Kola
25. Are Bolaji
26. Nasir Kwarra
27. Suleiman Barau Said
28. Abiodun Akinlade
29. Olufemi Lawrence Omosanya
30. Adeoye Abdulrazak Olalekan
31. Adeniyi Olowofela
32. Stephen A Jings
33. Wokocha Augustine
34. Abdullahi Aminu Tafida
35. Armaya’u Dauda Abubakar
36. Jibril Maigari
37. Saul Garba
38. Adamu Muhammad Sidi-Ali
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng