Cutar korona ta harbi mutane 34,000 a nahiyyar Afirka - WHO

Cutar korona ta harbi mutane 34,000 a nahiyyar Afirka - WHO

Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO, ta ce adadin mutanen da suka harbu da cutar korona a cikin awanni 24 da suka wuce a nahiyar Afirka ya karu daga mutum 33,000 zuwa sama da mutum 34,000.

Ofishin hukumar reshen nahiyar Afirka dake birnin Brazzaville a kasar Congo, shi ne ya sanar da hakan kan shafin na Twitter na @WHOAFRO a ranar Laraba.

Sanarwar ta bayyana cewa, akwai mutum 34,610 da cutar korona ta harba a nahiyar Afirka, yayin da sama da mutum 11,180 suka warke da kuma mutum 1,517 da ajali ya katsewa hanzari cikin kasashe 52.

Alkaluman WHO na reshen Afirka, sun nuna cewa cutar korona ta fi tsanani a kasar Afirka ta Kudu, a yayin da Kamaru da Ghana ke da mutum sama da 3,300 da cutar ta harba.

Taskar bayanai ta hukumar har ila yau ta nuna cewa, kasar Afirka ta Kudu, Algeria da kuma Kamaru su ne kasashen da cutar ta fi kamari a nahiyar.

Kididdigar alkaluman ta nuna cewa an samu mutuwar mutum 93 yayin da cutar ta harbi mutum 4,996 a kasar Afirka ta Kudu, sai kuma kasar Algeria da mutane 437 suka riga mu gidan gaskiya bayan mutum 3,649 sun kamu.

Alkaluman cutar korona a nahiyyar Afirka
Alkaluman cutar korona a nahiyyar Afirka
Asali: Twitter

Haka kuma kasar Kamaru da ta biyo baya na da mamata 58 bayan ta harbi mutane 1,702.

A taswirar alkaluman, kasar Mauritania, Gambia da Sao Tome and Principe, su ne kasashe uku a nahiyar Afirka da cutar korona ba ta yi wa illa ba sosai.

An samu mutum bakwai kacal da cutar ta harba a kasar Mauritania yayin da aka rasa ran mutum daya.

KARANTA KUMA: Tallafin $3.4bn da Najeriya za ta karba ba rance ba ne - IMF

A kasar Gambia kuma, an samu mutum goma da cutar ta kama da mutum daya da yasa ransa. Sai kuma Sao Tome and Principe inda aka samu mutane 11 masu cutar. Babu ko mutum daya da ya mutu a kasar.

Babu shakka kasar Najeriya ta kasance cikin jerin kasashe biyar da cutar korona ta fi yiwa barna a nahiyar Afirka.

Alkaluman hukumar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC sun nuna cewa, an samu karin mutum 195 da cutar ta harba a duk fadin kasar.

A halin yanzu dai Najeriya ta na da mutum 1,532 da cutar ta harba yayin da tuni mutum 44 sun ce ga garinku nan baya ga mutum 225 da suka warke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng