Babban sufetan Yansanda ya tura sabbin kwamishinoni zuwa Imo, Filato da Adamawa

Babban sufetan Yansanda ya tura sabbin kwamishinoni zuwa Imo, Filato da Adamawa

Babban sufetan Yansandan Najeriya, Muhammad Adamu ya bada umarnin tura sabbin kwamishinonin Yansanda zuwa jahohin Imo, Filato da Adamawa.

Sahara Reporters ta ruwaito mai magana da yawun rundunar Yansandan Najeriya, Frank Mba ne ya sanar da haka a ranar Talata, 28 ga watan Afrilu a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Mace mace a Kano: An tsinci gawar wani mutumi a karkashin gadar Kwankwasiyya

Sanarwar da Kakaaki Frank Mba ya fitar ta ce: “Babban sufetan Yansanda ya tura CP Olugbenga Adeyanju zuwa jahar Adamawa, CP Isaac Olutayo zuwa jahar Imo, CP Audu Adamu Madaki zuwa shelkwatar rundunar Yansanda dake Abuja, sai CP Edward Chuka zuwa Filato.”

Sanarwar ta bayyana cewa umarnin zai fara aiki ne nan take, don haka babban sufeta ya nemi al’ummar jahohin uku su baiwa sabbin kwamishinonin hadin kai.

Babban sufetan Yansanda ya tura sabbin kwamishinoni zuwa Imo, Filato da Adamawa
Babban sufetan Yansanda ya tura sabbin kwamishinoni zuwa Imo, Filato da Adamawa
Asali: Twitter

A hannu guda kuma, wasu gungun yan bindiga sun kashe wani jami’in rundunar Yansandan Najeriya mai mukamin Inspekta a garin Falwaya dake kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.

Yan bindigan sun kai harin kwantan bauna ne a kan wata motar Yansanda dake tafiya da yammacin Litinin, 27 ga watan Afrilu a kan hanyarsu ta zuwa Birnin Gwari.

Wani dan banga dake yankin, Hussaini Imam ya shaida ma Daily Trust cewa jami’in dansandan da aka kashe yana aiki ne a ofishin Yansanda dake Buruku, cikin karamar hukumar Chikun.

A wani labari kuma, Kungiyar ta’addanci ta ISWAP ta musanta ikirarin da shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya yi na cewa ya fatattake su daga yankin tafkin Chadi.

Jaridar Punch ta ruwaito kungiyar ta bayyana haka ne cikin wani bidiyo da ta saka inda ta nuna yadda ta yi ma jami’in Sojan kasar Chadi kisan gilla ta hanyar dirka masa harsashi a kai.

Jami’an gwamnatin kasar Chadi sun tabbatar da sahihancin bidiyon. Ko a cikin bidiyon an hangi mutumin da yan ta’addan suka kashe yana sanye da kakin Sojojin Chadi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel