COVID-19: Ganduje ya bayyana yadda cutar ke yaduwa a jihar Kano

COVID-19: Ganduje ya bayyana yadda cutar ke yaduwa a jihar Kano

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a jiya ya ce jihar na fuskantar babban kalubale sakamakon yadda annobar Covid-19 ke yaduwa. Hakan kuwa na bukatar taimakon gaggawa.

Gwamna Ganduje wanda ya yi jawabi yayin karbar kwamitin yaki da cutar Korona na fadar shugaban kasa a gidan gwamnati, ya ce jihar na cikin wani hali a kan cutar.

Ya ce: "Muna fuskantar kalubale daga kowanne bangare kuma muna bukatar taimako, ballantana yanzu da muka gane cewa a cikin garin ne sakamakon mu'amala cutar ke yaduwa."

Ganduje ya yi bayanin cewa, duk da yawan matakan da aka dauka don hana yaduwar cutar a jihar Kano, har yanzu jihar na fama da wasu al'adu da ke yada cutar.

A yayin jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bada umarnin rufe jihar gaba daya, gwamnan ya ce da an rufe dukkan kasar ne don samun sakamako mafi kyau, jaridar New Telegraph ta wallafa.

Ganduje ya ce rufe dukkan kasar da hana zirga-zirga zai iya kawo durkushewar tattalin arziki amma kuma hakan ne kadai zai kawo sakamakon da ake bukata.

Gwamnan ya matukar nuna damuwarsa ta yadda NCDC ta rufe dakin gwajin jihar. Ya ce hakan na iya kawo koma baya ga nasarar da aka fara samu a jihar.

COVID-19: Ganduje ya bayyana yadda cutar ke yaduwa a jihar Kano

COVID-19: Ganduje ya bayyana yadda cutar ke yaduwa a jihar Kano
Source: UGC

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnatin Kaduna ta gano makarantar da ake tura maza da mata almajiranci

"Ina maraba da kwamitin fadar shugaban kasa tare da jinjinawa kokarin shugaban kasar na kawo dauki da gaggawa. Jihar za ta bada hadin kai don yakar kwayar cutar.

"Ba za mu ce bamu da gogewar da za ta sa mu yaki cutar ba, amma muna fatan zuwanku ya karfafa mana guiwa don cimma manufarmu.

"Tuni mun tanadi matakan kariya, waraka da kuma tallafi don shawo kan kalubalen. Muna da cibiyoyin killacewa har uku tare da kwararrun ma'aikatan lafiya.

"Amma bayan rufe dakin gwajin da NCDC ta yi, ba dole bane kokarin ya kai ga cimma manufofinmu.

"A bangaren rufe jihar nan, muna bukatar jami'an tsaro da su saka tsauraran matakai na hana zirga-zirga. Don haka akwai bukatar mu kula da ma'aikatan lafiya tare da jami'an tsaro," Ganduje yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel