COVID-19: Gwamnatin Kaduna ta gano makarantar da ake tura maza da mata almajiranci

COVID-19: Gwamnatin Kaduna ta gano makarantar da ake tura maza da mata almajiranci

- Gwamnatin jihar Kaduna ta bankado makarantar da ake tura yara maza da mata almajiranci a karamar hukumar Zaria

- Kamar yadda kwamishinar walwala ta jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba ta ce, an samu yara mata 17 masu shekaru daga 8 zuwa 10 a cakude da maza

- Kwamishinar ta ce sun kwashe almajirai 327 daga makarantar Malam Aliyu Maikwari daga cikin 500 din da ya bai wa masauki a gidansa

Gwamnatin jihar Kaduna ta damke wani malamin tsangaya mai suna Aliyu Maikwari a karamar hukumar Zaria.

An zargi malamin ne da cudanya yara maza da mata don almajiranci, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin jihar ta kwashe almajirai 327 daga cikin 500 da ke gidansa inda ya basu masauki.

Kwamishinan walwala ta jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba, ta bayyana hakan ga manema labarai.

Ta ce daga cikin almajiran, akwai 17 duk yara mata ne masu shekaru 8 zuwa 10 kuma an cudanya su ne da sauran kattin almajirai maza a gida daya.

Ta bayyana cewa wannan ba koyarwar addinin Islama bace tare da dora laifin a kan iyayen yara matan da suka kai yaransu.

COVID-19: Gwamnatin Kaduna ta gano makarantar da ake tura maza da mata almajiranci
COVID-19: Gwamnatin Kaduna ta gano makarantar da ake tura maza da mata almajiranci
Asali: Facebook

KU KARANTA: COVID-19: Martanin jama'ar jihar Kano a kan hukuncin Buhari

"A lokacin da aka sanar dani, ban yarda ba sai da na ga hotunan yaran. Kananan yara mata wadanda shekarunsu bai wuce 10 ba aka hada da yara maza.

"Mun kwashe yara 327 daga cikin 500 da ke gidan. Saboda tsaurin idonsa, sai da muka hada da jami'an Operation Yaki kafin mu kama shi.

"Mun gano cewa yana aurar da kananan yaran da kansa. A halin yanzu ana bincikarsa a Kaduna," tace.

Ta ce an kama malamin ne a cikin kokarin gwamnatin jihar na mayar da almajirai garuruwansu don hana yaduwar cutar COVID-19.

A wani labari na daban, wasu mazauna birnin Kano sun bayyana goyon bayansu a kan dokar hana walwala da shugaban Buhari ya saka wa jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, a ranar Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada sanarwar rufe jihar saboda annobar Coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel