Bayan cutar Korona ta kashe mahaifin, bata-gari sun soka wa dansa wuka har lahira

Bayan cutar Korona ta kashe mahaifin, bata-gari sun soka wa dansa wuka har lahira

Wasu bata-gari sun yi nasarar halaka wani ma'aikacin NHS bayan kwanaki kadan da rasuwar mahaifinsa sakamakon barkewar annobar COVID-19.

David Gomoh mai shekaru 24 ya rasu ne bayan an soka mishi wuka a ranar Lahadi, sa'o'i kadan bayan ya bar gidansu da ke Newham a birnin London.

An kai wa David Gomoh hari ne a titin Freemasons da ke Custom House wurin karfe 10:25 na yammacin ranar Lahadi, 26 ga watan Afirilun 2020.

Kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, ya bar gidan lafiya kalau ba tare da yin wata muhawara da kowa ba.

Jami'an 'yan sandan da ke bincike a kan mutuwar matashin mai shekaru 24 sun ce babu wata alama daya da ke nuna fada aka yi da shi har aka kashe shi. Lamarin da yasa har yanzu ba a kama kowa ba.

Bayan kammala karatunsa daga jami'ar Southbank a fannin talla, David ya fara aiki da NHS.

A cikin kwanakin nan ne mahaifinsa ya rasu sakamakon cutar coronavirus.

Dan sanda mai bincike, Tony Kirk ya ce: "Yan uwan David na fuskantar matukar bacin rai. A cikin kwanakin nan ne suka rasa mahaifinsa sakamakon annobar COVID-19."

Bayan cutar Korona ta kashe mahaifin, bata-gari sun soka wa dansa wuka har lahira
Bayan cutar Korona ta kashe mahaifin, bata-gari sun soka wa dansa wuka har lahira
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Majalisar dattijai ta yi sabon kakaki

David matashi ne wanda ya ke aiki don samun biyan kudin makarantarsa har ya samu ya kammala. Mahaifiyarsa na aiki a NHS ne inda shima ya samu gurbi.

"Har a halin yanzu, mun yarda cewa wasu mutane ne suka tare David inda suka sossoka masa wuka har ya mutu," yace.

Ya kara da cewa, "Babu shakka shiryawa aka yi don halaka David, don shi kadai aka tare.

"David da mahaifiyarsa wadanda suka bada gudumawa mai yawa a yankin, suna bukatar taimakonku. A halin yanzu suna bukatar duk wanda ya san wani abu game da mutuwar David, da ya garzayo."

'Yan sandan sun gano cewa makasan David sun bar wurin ne a wata mota kirar Silver Dodge Caliber wacce aka bari a kan titin Lincoln da ke Plaistow.

An saci motar ne a Dagenham a ranar Alhamis, 16 ga watan Afirilu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel