Ganduje ya yi magana a kan tallafin covid-19 da Buhari zai bawa Kano

Ganduje ya yi magana a kan tallafin covid-19 da Buhari zai bawa Kano

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya yabawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a kan daukan matakan dakile yaduwar annobar cutar covid-19 a jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamna Ganduje ya yi korafin cewa gwamnatin tarayya ta yi watsi da jihar Kano yayin da take fama da annoba.

Amma, a cikin wani jawabi da kwamishinan yada labarai a jihar Kano, Muhammad Garba, ya fitar ranar Talata, ya bayyana cewa gwamna Ganduje ya yi murna da dokar rufe Kano na tsawon sati biyu da Buhari ya yi.

A daren ranar Litinin ne Buhari ya gabatar da jawabi ga 'yan Najeriya a kan halin da ake ciki dangane da yaki da annobar covid-19 a fadin kasa tare da sanar da daukan sabbin matakai a kan yanayin da ake ciki.

Buhari ya sanar da cewa gwamnatin tarayya ta tura wata tawagar kwararru da za su shawo kan annobar yawaitar mace-mace da annobar covid-19 da ake fama da ita a Kano.

A cewar kwamishinan, matakan da tarayya ta dauka tare da wadanda gwamnatin jiha ta dauka, zasu taimaka wajen samun raguwar yaduwar annobar coronavirus a Kano.

"Zuwan tallafin gwamnatin tarayya zai karawa kokarin gwamnatin jiha karfi wajen shawo kan annobar da ta balle a jihar Kano," a cewarsa.

Ganduje ya yi magana a kan tallafin covid-19 da Buhari zai bawa Kano
Ganduje da Buhari
Asali: Twitter

Ya kara da cewa duk da cibiyoyin gwajin hukumar NCDC da ke Kano sun dawo bakin aiki, gwamnatin jiha tana da shirin kara yawan cibiyoyin domin samun saukin yaki da kwayar cutar covid-19.

Kwamishinan ya bukaci jama'ar Kano su yi biyayya ga umarnin shugaba Buhari na rufe jihar na tsawon sati biyu.

Amma, jam'iyyar PDP ta yi zargin cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bai fadi wani abu da ya yiwa 'yan Najeriya dadi ba a cikin jawabin da ya gabatar kai tsaye da misalin karfe 8:00 na daren ranar Litinin.

DUBA WANNAN: Sheikh Yola da sauran manyan mutane uku da aka yi jana'izarsu a Kano ranar Talata

Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi ne domin sanar da 'yan Najeriya halin da ake ciki dangane da yaki da annobar covid-19 a fadin kasa tare da sanar da daukan sabbin matakai a kan yanayin da ake ciki.

A cikin jawabin da sakataren yada labaranta, Kola Ologbondiyan, ya fitar a daren ranar Litinin, PDP ta ce shugaba Buhari bai zo da wani abu sabo a cikin jawabinsa ba.

PDP ta ce Buhari ya kara jaddada dokar rufe jihohi ne kawai, amma ba tare da yin bayani a kan yadda za a taimaki jama'a da masana'antun da tattalin arzikinsu ya karye saboda dokar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel