Mace-macen Kano: Kwararrun likitoci sun isa, wasu sun tunkari jihar

Mace-macen Kano: Kwararrun likitoci sun isa, wasu sun tunkari jihar

Tawagar kwararrun likitoci sun dumfari jihar Kano da ke yankin Arewacin Najerriya sakamakon hali da jihar ke ciki.

A cikin mako daya, mutane da dama ne suka rasa rayukansu a cikin tsakiyar birnin Kano.

Kamar yadda Dakta Sani Gwarzo ya sanarwa BBC, kwararrun likitoci da yawa ne suka yi wa garin tsinke don tallafawa jihar wurin shawo kan tarin matsalolin da take fuskanta.

Hakan kuwa zai taka rawar gani wurin dakile yaduwar muguwar cutar Korona.

Kamar yadda yace, yanzu haka suna zagaya wuraren da aka yi tanadi don killace masu dauke da muguwar cutar Korona.

Hakazalika, suna zagaya cibiyar gwajin kwayar cutar da sauran wuraren kula da kiwon lafiya.

Kamar yadda wani dan majalisar wakilai mai wakiltar jihar Kano din ya shaidawa BBC, akwai wasu likitocin da ke hanyar shiga garin na Kano.

Da yawa kuwa daga cikin likitocin 'yan asalin jihar Kano ne.

Wannan na zuwa ne bayan jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na cewa zai aike wa jihar da tawaga domin gudanar da bincike.

Mace-macen Kano: Kwararrun likitoci sun tunkari jihar
Mace-macen Kano: Kwararrun likitoci sun tunkari jihar
Asali: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Martanin jama'ar jihar Kano a kan hukuncin Buhari

A wani labari na daban, Wasu mazauna birnin Kano sun bayyana goyon bayansu a kan dokar hana walwala da shugaban Buhari ya saka wa jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, a ranar Litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada sanarwar rufe jihar saboda annobar Coronavirus.

Shugaban ya ce: "A dangane da jihar Kano, na bada umarnin rufe ta gaba daya na makonni biyu tun daga yanzu.

"Gwamnatin tarayya za ta tura duk wani abu da ake bukata don shawo kai da hana yaduwar annobar zuwa jihohin da ke makwabtaka da Kano."

A tattaunawa ta daban-daban da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya yi da mazauna garin, sun bayyana cewa wannan babban ci gaba ne.

Habibu Umar, mazaunin yankin Rijiyar Zaki da ke birnin Kano, ya ce wannan hukuncin ne mafi cancanta ballantana wajen tsayar da yaduwar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel